Jahilci ne ya sa malamai suke karyata coronavirus - JNI

Mai alfarma Sarkin musulmi Sa'ad Abubakar na III

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar Musulman Najeriya ta Jama'atu Nasril Islam JNI karkashin jagorancin Sarkin Musulmai ta ce jahilci ne wani malamin addini ya fito yana ikirarin cewa coronavirus karya ce.

Kungiyar ta fitar da sanarwa ne ranar Litinin mai dauke da jan kunne ga malaman da sanarwar ta ce suna dulmuyar da al'umma kan cutar Covid-19 a Najeriya.

Sanarwar dai martani ce ga wasu malaman addinin Islama da suka fito suna wa'azi ga mabiyansu suna karyata cewa coronavirus karya ce makirci ne, cikinsu har da wasu manyan malaman da ke da'awa.

A cikin sanarwar da sakataren kungiyar JNI ya fitar Dr. Khalid Abubakar Aliyu, ya ce bai kamata irin wadannan kalamai su fito bakin duk wani malami ba da ya amsa sunansa malam.

BBC
BBC

Kungiyar ta ce abin takaici ne yadda wasu malamai ke wa'azi suna yaudarar al'ummar Musulmai kan ba su yadda da cutar coronavirus ba.

"Ya zama wajibi a matsayinmu na al'umma mu kaucewa duk wani abu da zai maimaita abin da ya faru a Italiya inda cutar ta yi kamari, saboda mutane sun bijerewa gargadin masana game da cutar."

Allah Ya ce Ka tambayi wadanda suka sani idan ba ka sani ba Q16:43, saboda haka ya kamata mu sani cewa ilimi amana ne wanda dole a kiyaye a gabatar da shi yadda yake."

Kungiyar ta nesanta kanta da abin ta kira karamin tunanin malamai game da duniya, wadanda ta ce rashin fahimtarsu babbar illa ce ga lafiya da zai jefa al'umma cikin hatsari.

Ta kuma kara da cewa ya kamata a fahimci cewa batun annoba ba sabon abu ba ne a tarihin duniya, inda ta ba da misalai da dama na abubuwan da suka faru a tarihi tun zamanin Sahabbai, da Tabi'ai wadanda suka gabace su.

Karin labaran da za ku so ku karanta

Sanarwar ta yi kira ga al'ummar Musulmai su yawaita Istigifari da neman gafarar Ubangiji.

Sannan a yawaita zikiri a ko da yaushe da kuma bayar sa sadaka da yawaita addu'o'i da karatun Al Qur'ani mai tsarki da kuma Sallar dare.