Coronavirus: Abu 65 da Buhari ya fada a jawabinsa ga 'yan Najeriya

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Buhari ya ayyana dokar hana fita a jihohin Abuja da Legas da Ogun, a jawabinsa na farko kan Coronavirus ga 'yan Najeriya

A karon farko, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi wa 'yan kasar jawabi game da matakan da gwamnatinsa ke dauka a yaki da coronavirus.

Muhimman abubuwan da ya fada sun hada da:

  • Saka dokar hana fita a Abuja da jihohin Legas da Ogun
  • Agaza wa mutanen karkara da ke kusa da Legas da Abuja
  • Daga wa wadanda suka ci bashin Tradermoni da MarketMoni da FarmerMoni kafa tsawon wata uku
  • An dauki ma'aikata na gaggawa don yakar coronavirus
  • Tura ma'aikatan lafiya zuwa tashoshin jiragen ruwa maimakon filin jirgin sama
  • Mayar da filayen kwallo da sansanonin alhazai wuraren killace masu dauke da coronavirus

Ga cikakken bayanin nasa kamar haka:

1. Tun daga alamun farko da ke nuna coronavirus ko COVID-19 ta zama annoba kuma aka ayyana dokar ta-baci a kanta, gwamnatin tarayya ta fara shiri na daukar matakai na kariya idan har cutar ta shigo Najeriya.

2. Hankalin gwamnati ya tattara ya koma kan tunkarar abin. Zuwa yanzu ta zama matsalar lafiya ta gaggawa da matsalar tattalin arziki.

3. Najeriya, abin takaici, ta tabbatar da bullar cutar a ranar 27 ga Fabrairun 2020. Tun lokacin kuma sannu a hankali muke samun karuwar wadanda suka kamu da cutar.

4. Daga safiyar 29 ga Maris 2020, jimillar wadanda suka kamu a Najeriya sun kai 97.

BBC
BBC

5. Abin bakin ciki, mun kuma samu mutuwar farko, tsohon ma'aikacin PPMC, wanda ya mutu ranar 23 ga watan Maris 2020.

6. Muna yi masa addu'a da jajantawa iyalinsa a wannan lokaci mai cike da kalubale. Muna kuma yin addu'ar fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka kamu da cutar kuma suke karbar magani.

7. Har zuwa yau COVID-19 ba ta da magani. Masana kimiyya na ci gaba da kokarin gano riga-kafi.

8. Muna tattaunawa da wadannan cibiyoyi a yayin da suke kokarin samar da mafita da hukumomi za su tabbatar cikin kankanin lokaci.

9. A yanzu, hanya ma fi dacewa ta kaucewa kamuwa da cutar ita ce bin matakai na tsafta da kuma nisanta da juna.

10. Mu kasance babban makami na yaki da wannan babbar annoba ta hanyar wanke hannu ko yaushe da sabulu da kuma ruwa mai tsafta, da tsaftace wuraren da muka yi amfani da su, yin tari ta hanyar rufewa da kyalle, ko tsakanin gwiwar hannu da kuma musamman kiyaye matakan kariya na lafiya da za mu iya kamuwa da cutar.

11. Tun da aka fara bayar da rahoton barkewar cutar a China, gwamnatinmu ke bibiyar al'amarin da nazari kan matakan da kasashe suka dauka.

12. Babban daraktan hukumar da ke yaki da cuttuttuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC, yana cikin mutum 10 manyan masu ruwa da tsaki a harkar lafiya da Hukumar Lafiya ta Duniya ta gayyata domin ziyartar China don lakantar irin matakan da suka dauka. Ina alfahari da Dr Ihekweazu da ya yi wannan aikin a madadin 'yan Najeriya.

13. Tun dawowarsa, NCDC ke daukar matakai da dama da shirye-shirye a Najeriya domin tabbatar da dakile tasirin cutar a kasarmu. Muna yin kira ga 'yan Najeriya su bayar da goyon bayansu ga ayyukan da Ma'aikatar lafiya da NCDC suke yi.

14. Ko da yake mun rungumi matakai da aka dauka a wasu kasashen duniya, amma an tsara shirye-shiryenmu daidai da yanayinmu.

15. A Najeriya muna daukar matakai guda biyu.

16. Na farko, mu kare rayukan 'yan Najeriya da kuma mazauna nan, na biyu, kare ma'aikata da 'yan kasuwa domin tabbatar da iyalinsu sun samu sauki cikin mutunci a wannan mawuyacin lokaci tare da kyakkyawan fata da kwanciyar hankali.

17. Zuwa yanzu, mun dauki matakai na kiwon lafiya da tsare kan iyakoki da matakai da suka shafi kudi. Kuma za mu ci gaba har abubuwa su daidaita.

18. Wadannan matakan ko shakka babu za su kawo cikas ga yawancin 'yan kasa. Amma wannan sadaukarwa ce da dukkaninmu za mu yi domin amfanin kasarmu.

19. A yaki da coronavirus, kowanne irin mataki muka dauka ba zai yi yawa ba kuma ba zai yi kadan ba. Maganar kawai ita ce ta daukar matakin da ya dace a lokacin da ya dace daga kwararrun ma'aikata.

20. Don Haka, a matsayinmu na gwamnati, za mu ci gaba da dogara da shawarwarin masana da kwararru a ma'aikatar lafiya da hukumar da ke kula da yaduwar cututtuka, NCDC, da sauran hukumomi a wannan lokaci na tsaka mai wuya.

21. Don haka, nake kira ga duka 'yan kasar nan da su bi dokokin da ake fitarwa a kai a kai.

22. Kamar yadda muka sani, Legas da Abuja ne wuraren da ke da mafi yawan mutanen da aka samu dauke da cutar a Najeriya. Don haka mun mayar da hankali wajen gaggauta dakatar da yaduwar cutar, kuma mu taimakawa sauran jihojin da yankuna iya karfinmu.

23. Shi ya sa ma muka samar da dala biliyan 15 don tallafawa 'yan kasa a lokacin da ake yaki da wannan cuta. 24. Mun kuma kaddamar da wani kwamitin shugaban kasa wato Presidential Task Force, don samar da wani tsari na matakan yaki da wannan cuta, wanda kuma ake bitarsa kullum. Wannan tsari ya kunshi hanyoyin da aka amince da su a fadin duniya amma mun tsara shi yadda zai dace da yanayin da kasarmu ke ciki.

25. Burinmu shi ne mu tabbatar duka jihoji na da goyon baya da karfin daukar matakai da gaggawa.

26. Kawo yanzu, a Legas da Abuja, mun dauki daruruwan ma'aikata na wucin gadi don kara karfin cibiyoyinmu na amsa waya da kuma tallafawa kokarinmu na gano mutanen da ake tunanin suna dauke da cutar da kuma wadanda aka yi wa gwaji.

27. Na kuma bukaci duka gwamnatocin jihohi, ta hanyar Kungiyar Gwamnonin Najeriya, da su tura likitoci da ma'aikatan jinya ga hukumar NCDC da gwamnatin jihar Legas domin horar da su kan hanyoyin hana yaduwar cutar ko da za ta yadu zuwa wasu jihohi.

28. Horon zai hada da wakilan bangaren lafiya daga dakarunmu da sauran jami'an tsaro da hukumomin leken asiri.

29. A matsayinmu na kasa guda, dole ne matakan da muke dauka su zama cikin tsari da kwarewa. Akwai bukatar samar da bayanan bai daya a fadin kasar. Za a kawar da duk wani bambanci a manufofi tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi.

30. Kamar yadda na fada a baya, kawo yanzu mutum 97 ne aka tabbatar suna dauke da cutar. Mafi yawansu a Legas da Abuja. Dukkansu suna samun kulawar da ta kamata.

31. Hukumominmu a yanzu haka suna aiki don gano wasu masu dauke da cutar da kuma mutanen da suka yi mu'amala da wadanda aka riga aka gano suna da cutar.

32. Kalilan daga cikin wadanda aka gano suna dauke da cutar a Legas da Abuja sun yi mu'amala ne da masu ita da suka yi tafiya.

33. Don haka muna aiki don tabbatar da cewa an dakatar da zirga-zirga tsakanin jihohi don hana ci gaba da yada cutar.

34. Duba da shawarar Ma'aikatar Lafiya ta tarayya da kuma NCDC, na bayar da umarnin hana duk wata zirga-zirga a Legas da babban birnin tarayya Abuja har tsawon kwana 14, daga ranar Litinin 30 ga watan Maris da 11:00 na dare. Wannan doka za kuma ta shafi jihar Ogun saboda kusancinta da Legas da kuma cunkoson da ake samu tsakanin jihohin biyu.

35. Ana umartar dukkan mazauna wadannan yankuna su zauna a gidajensu. A dakatar da tafiye-tafiye tsakanin garuruwa. A dakatar da dukkan harkokin kasuwanci tare da rufe ofis-ofis a wadannan garuruwa tsawon wannan lokaci.

36. Tuni an sanar da gwamnonin Legas da Ogun da kuma Ministan Birnin Tarayya. An kuma sanar da shugabannin hukumomin tsaro.

37. Za mu yi amfani da wannan dama wajen gano tare da killace dukkan wadanda suka yi mu'amala da mutanen da aka riga aka tabbatar sun kamu da cutar. Za mu tabbatar da cewa an kula da wadanda suka kamu a asibiti yayin da za mu takaita yaduwarta zuwa sauran jihohi.

38. Wannan dokar ba ta shafi asibitoci da sauran cibiyoyin lafiya ba da kuma wuraren da ake samarwa da rarraba magunguna ba.

39. Haka nan ba ta shafi wuraren kasuwanci ba kamar su;

a. Wajen sarrafa abinci da kamfanonin da ake sari;

b. Wuraren da ake rarraba man fetur da gidajen mai,

c. Kamfanonin rarrabawa da samar da wutar lantarki;

d. Haka zalika ban da kamfanonin tsaro masu zaman kansu

40. Duk da cewa dokar ba ta shafi wadannan wurare ba, to za takaita ziyarrtarsu kuma za a sa ido.

41. Za a bar ma'aikatan kamfanonin wayoyin salula da ma'aikatan watsa labarai - na rediyo da talbijin da jarida - wadanda suka tabbatar cewa ba za su iya aiki a gida ba, su je wuraren aikinsu.

42. Dukkan tashoshin jiragen ruwa da ke Lagos za su ci gaba da aiki kamar yadda dokoki suka tsara. Jami'an lafiyar da ke tashoshin jiragen ruwa za su binciki dukkan motoci da direbobinsu wadanda ke dauke da kayayyaki daga tashoshin jiragen ruwa zuwa wasu sassan kasar nan kafin su bar tashoshin.

43. Kazalika, za a binciki dukkan motocin da ke dauke da abinci da sauran kayayyakin agaji zuwa tashoshin jiragen ruwa daga wasu sassan kasar nan kafin a bar su su shiga wadannan killatattun wurare.

44. Haka kuma, an bayar da umarni ga Ministan Lafiya ya aika dukkan jami'an lafiya da aiki zuwa tashoshin jiragen ruwa wadanda a baya aka girke su a filayen jiragen saman Lagos da Abuja zuwa muhimman hanyoyi wadanda suka kasance mashiga da mafita daga wadannan killatattun wurare.

45. An dakatar da zirga-zirgar dukkan jiragen saman fasinja, na haya da kuma na masu kashin-kai. Za a bar su su yi amfani ne kawai idan akwai matukar bukatar hakan.

46. Muna sane cewa daukar wadannan matakai zai jefa 'yan kasa cikin kuncin rayuwa. Amma wannan batu ne na ko a mutu ko a yi rai, idan muka yi la'akari da mutanen da suka mutu a Italiya da Faransa da kuma Spaniya.

47. Don hakan, ya zama wajibi a gare mu mu kalli wannan batu a matsayin wani nauyi domin kare kasarmu daga yaduwar wannan cuta. Saboda haka ina yin kira ga dukkanmu da wannan batu ya shafa mu sarayar da jin dadinmu domin kare kanmu da sauran al'umma. Za mu kawar da wannan cuta ce kawai idan muka yi aiki baki daya sannan muka bi umarnin da masana kimiyya da masana harkokin lafiya suka yi mana.

48. A yayin da muka shirya domin tursasa wa mutane bin wadannan dokoki, ya kamata mu yi la'akari cewa wannan wata sadaukarwa ce da za mu yi wajen yaki da COVID-19. Kasashe da dama sun dauki matakan da suka fi namu tsauri wadanda suka ga amfanin su a kokarinsu na hana yaduwar wannan cuta.

49. Daga yanzu zuwa makonnin da ke tafe za mu bayar da kayan agaji ga mutanen da ke zaune a yankunan karkara da ke kusa da Lagos da Abuja wadanda za su fuskanci mawuyacin hali sanadiyar matakan da muka dauka.

50. Kazalika, ko da yake an rufe dukkan makarantu, amma na bayar da umarni ga ma'aikatar bayar da agajin gaggawa ta yi aiki da gwamnatocin jihohi domin samar da tsarin ci gaba da bayar da abinci ga 'yan makaranta a wannan lokaci ba tare da yin karan-tsaye ga dokar yi wa juna tazara ba. Ministar ma'aikatar bayar da agajin gaggawa za ta tuntubi jihohin domin su amince kan tsarin da za a bi wajen aiwatar da wannan tsari.

51. Haka kuma na bayar da umarni ba tare da wani bata lokaci ba da a daga wa masu biyan bashin kudin tallafi na Tradermoni da MarketMoni da kuma FarmerMoni kafa tsawon wata uku.

52. Na kuma umarci da a yi irin wannan sassauci ga dukkanin basukan da gwamnatin tarayya ta bayar ta hannun, Bankin Masana'antu da Bankin Manoma da kuma Bankin Shigarwa da Fitar da Hajoji daga Najeriya.

53. Ga wadanda ke amfani da kudaden basuka na abokanan huldarmu na duniya, na umarci cibiyoyinmu na kudaden Samar da ci-gaba da su tattauna da cibiyoyin na waje da suka bayar da bashin kan yadda za a sassauta wa wadanda aka ba wa bashin.

54. (Ga masu raunin da ake ba wa taimakon kudi na wata-wata don inganta rayuwarsu kuwa, na bayar da umarnin da a biya su na wata biyu na gaba. 'Yan gudun hijira ma za su samu tallafin kayan abinci na wata biyu a makonnin da ke tafe.

55. Muna kuma kira ga dukkan 'yan Najeriya Najeriya su dauki nauyin taimakawa wadanda ba su da wadata a cikin al'ummarsu ta hanyar taimakonsu da duk abin da za iya bukata.

56. A yayin da muke addu'ar samun mafita ta alkhairi, za kuma ci gaba da shiryawa duk wani abu da ka iya faruwa.

57. Wannan dalili ne ya sa na umarci a mayar da filayen kwallo da sansanin alhazai na gwamnatin tarayya su zama cibiyoyin killace marasa lafiya.

58. Ya ku 'yan Najeriya, a matsayinmu na gwamnati, za mu samar da dukkan abubuwan da ake bukata don kula da marasa lafiya. Za mu ci gaba da jajircewa don yin duk abin da za mu iya don tunkarar annobar COVID-19 a kasarmu.

59. Muna matukar farin cikin ganin yadda ake samun tallafi daga manyan 'yan kasuwa da kuma sauran abokan huldar muwajen dakile annobar nan.

60. A wannan gaba, zan bukaci a hada duk wata gudunmuwa ko tallafi waje guda don tabbatar da cewa an yi amfani da su ta hanyar da ta dace. Kwamitin shugaban kasa da ke yaki da COVID-19 ne zai ci gaba da zama mai tsara duk abin da ya shafi annobar.

61. Ina so na tabbatar muku cewa dukkan ma'aikatun gwamnati da hukumomin da suke da rawar da za su taka suna aiki tukuru don shawo kan wannan annobar.

62. Kowace kasa ta duniya na fuskantar kalubale a wannan lokaci. Amma mun ga kasashen da jama'arta suka taimaka wajen rage yaduwar cutar.

63. Don haka zan ci gaba da kira a gare ku da ku bi dokokin da aka sanya kuma ku yi naku kokarin wajen bai wa gwamnati hadin kai da kuma taimakon marasa karfi a al'ummarku.

64. Zan yi amfani da wannan damar na godewa cibiyoyin lafiyarmu da ma'aikatan lafiya da hukumomin da ke kula da gabar teku da sauran ma'aikatan da aikinsu ya zama wajibi a kowane yanayi domin jajircewarsu da sadaukarwarsu. Lallai kun cika gwaraza.

65. Na gode muku duka da saurarata da kuka yi. Allah Ya ci gaba da yi mana albarka da kare mu duka.