Na kamu da coronavirus – Nasir El-Rufai

Asalin hoton, Kaduna State Government
Gwamnan iihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce ya kamu da annobar coronavirus, wadda ke haddasa cutar Covid-19.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wani gajeren jawabi da ya yi a wani bidiyo da fadarsa ta wallafa a shafin Twitter ranar Asabar.
Kazalika ya ce har yanzu bai fara nuna alamun cutar ba amma ya killace kansa.
"A farkon makon nan ne na yi gwajin cutar Covid-19, kuma sakamakon ya fito a yammacin yau. Ina mai bakin cikin shaida muku cewa ina dauke da cutar," in ji El-Rufai.
"Kamar yadda hukumomin lafiya suka tsara kan abin da mai dauke da cutar ya kamata ya yi, na killace kaina. Mataimakin gwamna zai ci gaba da jan ragamar kwamiti na musamman kan Covid-19 sannan zan ci gaba da bayar da bayanai lokaci zuwa lokaci."
Nasir El-Rufai ya yi kira ga al'ummar jihar Kaduna su ci gaba da bin dokar da gwamnatinsa ta kafa a jihar da kuma shawarwarin hukumomi domin kare kansu daga Covid-19.
Wannan na zuwa ne 'yan sa'o'i da gwamnatinsa ta bayar da sanarwar cewa ta kama wasu malamai guda biyu bisa saba dokar hana taruka da suka yi, inda suka jagoranci sallar Juma'a a masallatansu.
An kama malaman ne a Malali da Unguwar Kanawa da ke birnin na Kaduna.
Zuwa lokacin rubuta wannan rahoto hukumomi ba su bayar da sanarwar samun mai dauke da cutar ba a Kaduna sai gwamna El-Rufai kadai, wanda ya sanar da kansa.
Zuwa karfe 4:00 na yammacin Ranar Asabar, mutum 89 ne hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa ta tabbatar sun kamu da coronavirus a Najeriya.
Ga jerin jihohin da cutar ta bulla:
Legas - 59
Abuja - 14
Ogun - 3
Enugu - 2
Ekiti - 1
Oyo - 3
Edo - 2
Bauchi - 2
Osun -1
Rivers -1
Benue - 1













