Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: An dakatar da jiragen kasar waje a Abuja da Lagos
Gwamnatin Najeriya ta rufe filayen jirgin sama na Abuja da Legas bisa la'akari da yadda annobar coronavirus ke ci gaba da yaduwa kamar wutar daji.
Yanzu haka dai kididdigar hukumar da ke hana yaduwar cututtuka ta kasar ta nuna an samu mutum 40 da aka hakkake sun kamu da wannan annoba.
Wannan rufewar dai ta shafi tashi da saukar jiragen da suke zuwa daga kasashen waje ne kawai, inda za a ci gaba da gudanar da zirga-zirgar cikin gida.
A makon da ya gabata ne dai hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar ta sanar da rufe filayen guda biyu da ta ce za a yi ranar Litinin.
A wata sanarwa da babban darektan hukumar, Kaftin Musu Nuhu ya sanya wa hannn, hukumar ta ce rufe filin jirgin Abuja da Legas kari ne a kan rufe filin jirgin Kano da na Enugu da kuma na Fatakwal wadanda suka hanyoyi ne da annobar ka iya shiga kasar ta cikinsu.
A ranar Asabar din da ta gabata ne dai hukumar ta rufe na Kano da Enugu da kuma Fatakwal.
Nuhu ya kara da cewa rufe filayen jirgin zai kasance har zuwa ranar 23 ga watan Afrilu, sai dai ya ce za a iya sauka da tashi a yayanyin bukatar gaggawa a dukkanin filayen jiragen.