Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: 'Yar Buhari ta killace kanta bayan dawowa daga London
Uwargidan Shugaba Buhari Aisha ta sanar da cewa 'yarta ta killace kanta bayan komawarta Najeriya daga Birtaniya inda coronavirus ta fara yawa a can.
A wasu jerin sakonni da ta wallafa a shafinta na Twitter, Aisha Buhari ta ce a ranar Alhamis ne 'yar tata wacce ba ta fadi sunanta ba ta koma Najeriyar daga Birtaniya.
Ta ce yarinyar ta killace kan nata ne saboda shawarar da Ministan Lafiya na kasar suka bayar ba wai don ta nuna alamun cutar ba.
Kuma ta yi kira ga iyaye su dauki iirn wannan matakin idan yaransu sun dawo daga tafiya.
Kazalika uwargidan shugaban kasar ta ce ta rufe ofishinta na tsawon mako biyu saboda wasu ma'aikatan ofishin nata sun dawo daga Birtaniya.
Aisha Buhari ta kuma yaba wa gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya bakwai da na jihar Neja da Kwara kan matakan da suka dauka na dakile yaduwar cutar.
Ta kara yin kira ga mutane da su ci gaba da bin shawarwarin jami'an lafiya don kauce wa yaduwar cutar.