Buhari da Atiku sun yaba wa kungiyar Izala

Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Ikamatis Sunnah wato JIBWIS ta gudanar da babban taronta na shekara-shekara tare da wa'azi da kuma kaddamar da gidauniyar neman taimako a Abuja babban birnin Najeriya.

Kungiyar ta JIBWIS ta ce manufar kaddamar da asusun neman taimakon na naira miliyan 285 ita ce, gina karin manya da kananan makarantu da kayan aiki kamar kwamfyutoci da motoci da dai sauransu domin ilimin addinin Musulunci da na boko a kasar.

A lokacin taron da ya gudana a Tsohon Filin Fareti na Kasa wato Old Parade Ground da ke Abuja, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaba wa kungiyar ta Izala saboda abin da ya kira addu'o'in alheri suke yi wa gwamnati da kuma kasa baki daya, gami da shawarwari kan yadda za a inganta tafiyar da gwamnati.

Shugaba Buhari dai shi ne babban bako na musamman amma bai samu halartar taron ba.

To sai dai ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, ya wakilce shi ya kuma gabatar da sakonsa na godiya da fatan alheri.

Wani abu da ya dan dau hankali a taron shi ne ministan ya sanar da cewa Shugaba Buhari ya ba shi sakon 'miliyoyin naira' ga kungiyar Izala a matsayin gudummuwarsa ta kashin kansa, amma bai bayyana takamaimai adadin kudin ba, domin shugaban ya umarce shi da kada ya fada a bainar jama'a.

Shi ma tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma wanda ya yi wa babbar jam'iyyar adawa ta PDP takarar shugabancin kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, bai samu halartar taron ba duk da cewa JIBWIS ta gayyace shi a matsayin babban bako.

To sai dai wani na hannun damarsa Honorouble Shehu Buba, ya wakilce shi inda ya sanar da bayar da gudummowar kudi naira miliyan biyar ya kuma yaba da yunkurin JIBWIS na karfafa ilmi a fadin Najeriya.

Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa ta Kungiyar JIBWIS Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya ce kawo yanzu kungiyar ta gina makarantu fiye da 4000 a fadin Najeriya, kuma wannan gidauniyar da aka kaddamar na da nufin fadada ayyukan ilmi ne.

Dangane da matsalar tsaro a Najeriya kuwa, Sheikh Jingir ya ce ko da yake har yanzu akwai sauran matsalar tsaro amma munin lamarin bai kai na shekarun baya ba sakamakon kokarin da hukumomi ke yi.

Ya ce akwai bukatar kara hada gwiwa tsakanin jama'ar kasa da gwamnati domin kyautata lamarin tsaro da ilmi.

Kungiyoyin addinin Islama a Najeriya dai kan sha suka saboda yadda ake zargin suna sako-sako da gina manyan makarantu musamman jami'o'i don bunkasa ilmi mai zurfi, to amma kungiyar ta JIBWIS ta ce yunkuri na baya-bayan nan akwai batun gina manyan makarantun ilmi mai zurfi.

Taron ya samu halartar dubban jama'a daga sassa daban-daban na Najeriya musamman arewacin kasar.