Yadda El-Rufa'i ya raka Sanusi har kofar jirgin Legas

Asalin hoton, @GovKaduna
Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya koma Legas da zama bayan shafe kwana biyu a jihar Nasarawa.
Sarki Sanusi ya bar kauyen Awe a jihar Nasarawa tare da rakiyar gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'I wanda ya raka shi har kofar jirgin da ya shiga zuwa Legas a Abuja.
A ranar Juma'a ne wata Kotu a Abuja ta bayar da umurnin bai wa tsohon Sarkin na Kano damar shiga ko ina a Najeriya ban da jihar Kano.
Lauyoyin tsohon sarkin ne suka shigar da kara suna kalubalantar abin da suka kira tauye masa hakkin walwala da kundin tsarin mulki ya ba shi bayan tsare shi a kauyen Loko kafin a mayar da shi garin Awe a jihar Nasarawa.
Hotunan da gwamnatin jihar Kaduna ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Juma'a, sun nuna yadda gwamna El Rufa'i ya raka Sarki Sanusi har kofar jirgin da ya hau zuwa Lagos.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1

Karshen labarin da aka sa a X, 2
Sannan gwamna El Rufa'I da Sarki Sanusi mota daya suka shigo tun daga jihar Nasarawa har zuwa Abuja.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Tun da farko shafin Twitter na gwamnatin Kaduna ya wallafa hotunan yadda gwamna El Rufa'I ya isa garin Awe domin Sarki Sanusi da aka tube.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Kafin ya baro garin Awe, tsohon Sarkin na Kano ya gabatar da huduba tare da jagoranci Sallar juma'a da harshen Larabci da kuma Hausa.
A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kano ta Abdullahi Umar Ganduje ta cire Sarki Sanusi na II daga kan mulki bayan ta zarge shi da rashin biyayya da kuma kin bin umarnin gwamnan jihar.
Cire Sarkin daga gadon sarautar Kano da kuma tura shi jihar Nasarawa ya janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya.