Sarki Sanusi ya samu 'yanci zai tafi Legas

Asalin hoton, EL-Rufa'i Twitter
Sarki Sanusi ya samu 'yanci zai tafi Legas.
Majiya mai karfi ta tabbatar wa da BBC wannan batu, inda ta ce a yanzu tsohon Sarkin zai gabatar da Sallar Juma'a a garin Awe kamar yadda mutanen garin suka bukata.
Daga na ne kuma shi da gwamnan jihar Kaduna za su tafi Abuja inda daga nan zai kama hanyar zuwa Legas.
Wannan dai ya biyo bayan umarnin da wata babbar kotu a Abuja ta bayar na cewa a bai wa Muhammadu Sanusi damar shiga ko ina a Najeriya ban da Kano.
A hudubar da sarkin yake yi a garin Awe gabanin Sallar Juma'a, ya yi magana a kan imani da kaddara dakuma hikimomin Ubangiji wajen shirya abubuwa.
Sarkin ya janyo ayoyi da hadisai da suke nuna muhimmancin yarda da kaddara.
"Duk abin da Allah Ya kaddara wa mutum to lallai akwai alkhairi a cikinsa,
Tuni gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i ya dauko tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi daga garin Awe, inda suka durfafi Abuja.
Ana sa ran tsohon sarkin zai wuce Legas daga Abuja nan gaba.











