Buhari ya ce a hukunta jami'an da ke yi wa gwamnatinsa zagon kasa

Asalin hoton, @buharisallau
Shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ya ba da umarnin hukunta jami'an da ke da hannu a batan dabon motocin man fetur 295 da aka kama a iyakokin kasar.
Tun da farko shugaban ya sa ofishin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro ya yi cikakken bincike a kan yadda jami'an da ke da alhakin tsare iyakokin kasar suka saki motocin ba tare da izini ba.
Binciken ya bankado yadda wasu jami'an gwamnati suka hada baki wurin sakin motocin da kuma abin da ya ce zagon kasa ne ga shirin gwamnatin na rufe iyakokinta ga 'yan fasa-kwaurin kan tudu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Buhari ya ba da umurnin maye gurbin dukkan masu hannu a bacewar motocin a iyakokin kasar nan take. Ya kuma umurci ma'aikatunsu da su yi musu horo mai tsanani.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Sanarwar da fadar shugaba ta fitar ta ce shirin tsarin rufe iyakokin kasar na kan tudu ya yi nasarar kwace kaya da suka hada da kayan abinci da tufafi da albarkatun mai da ma'adinai da aka yi nufin fasa-kwaurinsu zuwa Najeri
Ya kuma yaba wa jam'ian tsaro bisa jajircewarsu a kan ayyukansu.