Coronavirus: Atiku ya bai wa Buhari shawara kan yadda za a yaki cutar

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar tare da shugaba Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP mai hamayya ya ba gwamnatin Buhari shawarwari ciki har da soke jigilar jirage zuwa kasashen da cutar ta bulla.

A cikin wasu jerin sakwannin da ya wallafa a Twitter, Atiku ya ce yanzu da aka tabbatar da bullar coronavirus a Lagos, a matsayinsa mai kishin kasa zai ba gwamnatin Buhari shawara kan matakan da suka fi dacewa a dauka.

A ranar Alhamis ne hukumomi a Najeriya suka tabbatar da bullar cutar corona a Najeriya inda suka ce wani dan Italiya ne da ke aiki a kasar ya shigo da cutar bayan ya dawo daga Milan zuwa Lagos.

Atiku wanda ya sha kaye zaben 2019 kuma babban mai hamayya da Buhari, ya ce kamar yadda aka rufe iyakoki domin yakar zagon kasa ga tattalin arzikin kasa, yanzu kuma lokaci ne da ya dace a dakatar da jigilar jiragen sama zuwa kasashen da ke fama da cutar.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

"Najeriya na bukatar daukar tsauraran matakai domin dakile bazuwar cutar. kuma kare rayuka ya fi ceto tattalin arziki muhimmanci"

"Yanzu babu wani batun zargi ko nuna dan yatsa ga wani. Idan ana zargi ya kamata a dakata, a mayar da hankali wajen samar da mafita." in ji Atiku.

corona
corona

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kara bayar da shawarar cewa ya kamata a nemo kwararrun da suka yaki cutar Ebola lokacin da ta bulla Najeriya a 2014.

A cewarsa gwamnatin da ke mulki a lokacin ta yi aiki ne tare da gwamnatocin jihohin Lagos da Rivers. Kuma a cewarsa hadin kan da aka samu kan manufa daya shi ya taimaka aka dakile cutar.

Atiku ya yi kira ga 'yan Najeriya su kwantar da hankalinsu. "Mun yaki Ebola, za mu iya yin galaba kan wannan halin da muka shiga."

Cutar corona dai yanzu an bayyana cewa ta yadu zuwa kasashe fiye da 50. Kuma Najeriya ce kasa ta uku da cutar ta bulla a nahiyar Afirka.

corona