Kalli yadda asibitin cutar Coronavirus yake a Legas
Latsa bodiyon sama domin kallo
Ziyarar da BBC ta kai asibitin da aka ware na musamman domin magance yaduwar cutar COVID-19 a birnin Legas a Najeriya.
A ranar Juma'a 28 Fabrairu 2020 ne gwamnatin Najeriya ta sanar da bullar cutar a kasar.
COVID-19 ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a duniya tun bayan bullarta a watan Disamban 2019 a kasar China.
Zuwa yanzu an samu bullar cutar a kasashe sama da 50.
Najeriya ce kasar farko da aka samu bullar cutar a kasashen da ke Kudu da Hamadar Sahara.
Wasu kasashe sun hana shigowar baki daga wuraren da ke fama da cutar.
Annobar ta kuma sa hukumomi killace wasu garuruwa da makarantu da taruka domin dakile yaduwarta.