Najeriya ta tabbatar da bullar Coronavirus a Lagos

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da bullar cutar coronavirus da ake kira Covid-19 a jihar Lagos.
Ma'aikatar lafiya ce ta tabbatar da bullar cutar a sanarwar da ta wallafa a Twitter, inda ta ce a karon farko an samu bullar cutar a Najeriya tun barkewarta a China a watan Janairun 2020.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Haka ma cibiyar da ke yaki da cututuka masu yaduwa a Najeriya ta wallafa a Twitter inda ta ce ministan lafiya ya tabbatar da bullar cutar a jihar Lagos.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
A sanarwar da ya fitar, ministan lafiya na Najeriya Dr Osagie Ehanire ya ce wani dan Italiya ne da ke aiki a kasar ya shigo da cutar bayan ya dawo daga Milan zuwa Lagos.
"Sakamakon gwaji da aka gudanar a asibitin koyarwa na jami'ar Lagos ya tabbatar da yana dauke da cutar."
"Ana duba lafiyarsa a asibitin kula da cutuka masu yaduwa a Yaba, kuma marar lafiyar bai nuna alamomi masu muni ba," in ji shi.
Ya kuma ce gwamnati ta kara tsaurara matakai domin tabbatar da dakile yaduwar cutar.
Tun a ranar Laraba ne ake ta yada jita-jitar labarin bullar cutar a Lagos a shafukan intanet bayan kwantar da wani dan China a asibitin Reddington da ke Ikeja.
Daga baya asibitin ya karyata labarin amma bai musanta zuwan dan China ba a asibitin domin diba lafiyarsa da ake fargabar yana dauke da cutar mai yin kisa a China.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce cutar coronavirus ta kai wani matsayi na zama annoba a duniya saboda yadda take yaduwa.
Najeriya yanzu ta shiga jerin kasashen duniya da aka samu bullar cutar ta da ake kira COVID-19, kasa ta uku da aka samu bullarta a Afirka bayan Masar da Aljeriya.











