Coronavirus tips: Yadda za ku kare kanku daga kamuwa da coronavirus

Mun soma wallafa wannan labari a watan Fabrairu, 2020.

A yayin da cutar korona ke ci gaba da yaduwa a duniya, hukumomin lafiya sun shawarci mutane kan yadda za su kare kawunansu.

Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta ce mutane da dama da suka kamu da cutar sun fara ne da kananan cututtuka.

WHO ta ce za ku iya kare kawunanku idan kuka bi wadannan matakan.

Yadda za ku kare kawunanku

  • Wanke hannu a ko yaushe: Ku wanke hannayenku akai-akai da ruwa da sabulu.
  • Guji matsawa kusa da mutumin da ke tari da atishawa. Akalla ya kasance akwai tazarar mita daya tsakaninku.
  • Daina taba idanu da hanci da baki - idan kuka yi taba abubuwa da yawa da hannayenku, za ku iya kamuwa da cutar. Da zarar kun tabo kwayoyin cutar da hannayenku to za ku iya bazawa a bakunanku da idanuwanku. Daga nan kwayar cutar za ta shiga jikkunanku ta sanya ku rashin lafiya.
  • Gwajin jan numfashi - ku rufe bakinku da hancinku da gwiwar hannunku idan za ku yi tari ko atishawa.
  • Idan kuna zazzabi ko tari kuma ba kwa iya jan numfashi da kyau, to ku hanzarta ku ga likita.
  • Ku nemi karin bayani ku kuma bi shawarwarin likita.

Cibiyar Yaki da Cututtuka ta kuma shawarci mutane kanyadda za su kare kawunansu daga hadarin yaduwar cutar.

  • Wanke hannayenku da kyau a bakin famfo.
  • Rufe bakunanku da hancinku sosai da hankici ko tolifefa idan kuna tari ko atisahwa. Za kuma ku iya yin tarin a gwaiwar hannunku.
  • Guji sayen magani ba tare da umarnin likita ba. Idan ba ku da lafiya, ku ziyarci asibiti mafi kusa da ku.
  • Ma'aikatan lafiya su bi matakan hana kamuwa ko yaduwar cututtuka yayin duba marasa lafiya.
  • Mutanen da suka dawo daga Chana ba tare da nuna alamar cutar ba, amma daga baya cikin kwana 14 suka fara tari ko zazzabi su tuntubi NCDC.

Cibiyar Gwajin Ingancin Abinci ta Ghana ta bayar da shawarwarin kare kai daga kamuwa da coronavirus.

Dokta Bashir Boi-Kikimoto, ya ba wa 'yan kasar wadannan shawarwari guda hudu:

  • Wanke hannu da sabulu da ruwa.
  • Tanadi sunadarin wanke hannu da kyallen goge hannu domin tabbatar da tsaftar hannu a koyaushe.
  • Nisanci cin naman dabbobin dawa. Bincike ya nuna cewa sunadarin Amino Acid 500-1000 da coronavirus ke dauke da shi an samo shi ne daga dabbobi, musamman na dawa.
  • Guji amfani da magungunan gargajiya da ake hadawa daga sassan jikin namun daji.

Ya kuma ba wa gwamanti shawarwari:

  • Tsaurara hanyoyin shiga kasar: Jiragen da ke shiga kasar su rika mika takardun bayanan da fasinjoji suka cika. Hakan zai bayar da dama hukumomi su yi saurin tantance wadanda suka samu kusanci da cutar.
  • A inganta matakan kula da lafiya a tashoshin jiragena kasar ta yadda za a yi saurin gano masu dauke da cutar a iyakokin kasar.
  • Ma'aikatan lafiya su rika sanya kayan kariya domin kauce wa cudanya da cutar yayin gudanar da ayyukansu.
  • A mayar da cibiyoyin cutar Ebola biyu da ke kasar zuwa cibiyoyin coronavirus tun da Ebola ba ta shiga kasar ba.
  • Wayar da kai: Jami'an lafiya su rika wayar da kan 'yan kasa game da hanyoyin hana yaduwa da kare kai daga kamuwa da kwayar cutar mai kisa.

Mutum fiye da 80,000 na iya kamuwa da cutar coronavirus da ta fara bulla a birnin Wuhan na kasar China.