Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cutar coronavirus: 'Yan matan da suka ƙirƙiro na'urar taimaka wa masu korona yin numfashi
Wasu mata a Afghanistan sun kirkiro na'ura mai rahusa da ke taimaka wa masu fama da cutar korona yin numfashi.
Matasan matan suna fatan asibitoci za su rika amfani da wannan na'ura kuma za a kawar da matsalar karancin na'urorin taimaka wa masu fama da cutar yin numfashi.