EFCC ta yi tattaki don yaki da cin hanci a Ranar Valentine

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'anati tana tattaki a duk fadin kasar ranar Juma'a domin wayar da kan jama'a game da illar cin hanci da rashawa.

EFCC ta shirya hakan ne albarkacin Ranar Valentine, wato ranar masoya ta duniya.