Yadda aka yi wa Buhari ihu a yayin ziyararsa a Maiduguri

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin Borno na cewa an yi wa Shugaba Muhammadu Buhari ihun ''ba ma yi, ba ma yi'' yayin ziyarar da ya kai yau Laraba.
Wasu kwararan majiyoyi sun tabbatar wa BBC faruwar lamarin.
Hakan kuma ya faru ne lokacin da Buhari yake barin fadar Shehun Borno zuwa gidan gwamna a wani waje da ake cewa 'Yan Nono.
Buhari dai ya ziyarci Maiduguri ne domin jajanta wa gwamnati da al'ummar jihar bisa hare-haren da Boko Haram ta kai kan wasu matafiya abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Tuni wani bidiyo da ake masa ihun ya bazu tamkar wutar daji a shafukan sada zumuntar Najeriya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Sannan sunan Buharin na daga cikin mafiya tashe a shafukan a yau Laraba.

Buhari ya sha alwashin samar da tsaro a Najeriya
Jim kadan bayan samun rahotannin ihun da aka yi masa din, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya jaddada alkawarinsa na inganta tsaro a fadin kasar.
Buhari ya bayyana haka ne bayan ziyarar ta'aziyyar da ya kai jihar Borno domin jajanta wa gwamnati da jama'ar jihar game da kashe mutum kusan 30 da kungiyar Boko Haram ta yi.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan ziyarar, Buhari ya ce:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
"Ina tabbatar wa dukkan 'yan Najeriya cewa muna daukar matakan inganta tsaro a fadin kasar.
"A jihar Borno, sojoji za su ci gaba da aiki tukuru domin magance masu tayar da kayar baya.
Ina rokon shugabannin al'umma da jama'a da su taimaka wa sojoji da bayanai da goyon baya da ya dace."

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya isa Maiduguri babban birnin jihar Borno bayan ya dawo daga Addis Ababa a ranar Laraba.
Mai bai wa shugaban kasar shawara kan kafafen yada labarai Garba Shehu ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.
Ya ce Buhari ya je ne domin yin ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar Borno kan harin ta'addancin da aka kai jihar a baya-bayan nan.
Harin wanda Boko Haram ta kai ya halaka matafiya da dama ciki har da wadanda 'yan kungiyar suka cinna wa wuta a cikin mota.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3

Karshen labarin da aka sa a X, 4
A sakon ta'aziyyarsa bayan harin na ranar Lahadi, shugaban kasar ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta kare rayuka da dukiyoyin 'yan kasar.
Shugaban tare da tawagar Najeriya da ke halartar taron kungiyar Tarayya Afirka a kasar Habasha a lokacin sun yi shiru na minti daya domin juyayin wadanda aka kashe a harin, gabanin ganawarsa da 'yan Najeriya mazauna Habasha.

Asalin hoton, @BashirAhmaad
An caccaki Buhari
An shafe kwana uku ana caccakar shugaban kasar a shafukan sada zumunta da muhawara na kasar, inda aka dinga sukar sa da gazawa a harkar tsaro.
Ga wasu daga cikin sakonnin da 'yan kasar suka yi ta wallafawa a shafukan sada zumuntar:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 5
Shugaban kasa ka ba da yawa daga cikinmu kunya saboda ba ka yin abin da ya kama," a cewar Justice Naseer.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 6
Zamdai Marcel Sunny ya ce "ya kamata a ja wa sojoji kunne cewa su kasance cikin shiri a ko yaushe."