Zulum ya bai wa Buhari shawara kan Boko Haram

Asalin hoton, @Buharisallau1
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya shawarci shugaba Muhamamdu Buhari da ya sauya dabarar yaki da kungiyar Boko Haram.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau ya fitar, ta ce Zulum ya bayyana haka ne yayin karbar bakuncin Buhari a ziyarar ta'aziyya da ya kai a fadar Shehun Borno Abubakar Umar El-Kanemi.
Ziyarar ta zo ne bayan harin kungiyar Boko Haram da ya yi sanadiyya mutuwar mutum 30 da kona motoci da gidaje a garin Auno.
Gwamnan ya koka game da karuwar hare-haren kungiyar da suka salwantar da rayuka da dukiyoyi tun a farkon shekarar 2019.
"Shugaban kasa daga watan Maris na 2019 zuwa yanzu hare-haren 'yan bindiga sun karu tare da jawo asarar rayuka da dukiyoyi," Gwamna Zulum ya fada wa Shugaba Buhari.
"Muna kira ga sojoji da su sauya salonsu na yaki kuma muna iya amfani da manyan nasarorin da sojojinmu suka samu a 2016 zuwa 2017 domin kawo karshen tayar da kayar baya.
"Akwai bukatar kai yakin zuwa mafakar mayakan a yankin tabkin Chadi da dajin Sambisa da sauran wurare", inji gwamnan.
Sanarwar ta ce gwamnan ya yaba wa Buhari bisa dagewarsa wurin yakar ayyukan kungiyar da kuma yadda yake nuna damuwa a kan halin da mutanen jihar ke ciki.
Da yake yaba nasarorin da aka samu wajen yaki da Boko Haram a 2016 zuwa 2017 sanda aka murkushe kunigyar a kusan kananan hukumomi 20 a jihar, gwamnan ya nuna takaicinsa game da sake dawowar hare-haren kungiyar a baya-bayan nan.
A nasa bangare shugaba Buhari ya jaddada aniyarsa ta kawo karshen ayyukan Boko Haram da yaki da almundahana da kuma farfado da tattalin arzikin kasar.
Buhari ya kuma bukaci jama'ar jihar Borno da su ci gaba da bai wa sojoji goyon baya.










