An gurfanar da manoman shinkafa gaban kotu a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da takaddama kan wani shiri na bai wa manoma bashi don bunkasa noman shinkafa a Najeriya.
Kungiyar manoma shinkafa ta kasar RIFAN, ta yi ikirarin cewa an gurfanar da 'ya'yanta 70,000 a gaban kotun majistare saboda sun ci bashin kudin noman shinkafa kuma ba su biya ba.
To sai dai wasu 'yan adawa a kasar na cewa tun farko ba manoma aka bai wa kudin ba, wasu 'yan koran siyasa aka ba wa shi yasa mutane suka ki biya.
Kungiyar manoman shinkafar a jihar Kebbi ta ce an gurfarnar da dubban manoman shinkafar ne a gaban kotuna bayan sun karbi bashin kudi daga shirin Babban Bankin Nijeriya na bunkasa noma wato Anchor Borrowers wanda aka fara a shekara 2015.
Shugaban kungiyar shinkafa na jihar Kebbi Alhaji Muhammadu Sahabi, ya ce hukumomi sun dauki matakin gurfanar da 'ya'yan kungiyarsa ta RIFAN ne saboda sun kin biyan basukan da suka ci.
Tun da farko, jam'iyyar PRP mai adawa a jihar Kebbi ce ta nemi jin bahasin inda aka kwana game da kudin da gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 17 na bunkasa noman shinkafa.
Jam'iyyar ta ce babu wani abun a zo a gani duk da makudan kudin da aka ware.
Ana dai fargabar cewa irin wannan shiri da hukumomi a kasar suka bullo da shi don bunkasa noma a cikin gida da wadata kasar da abinci, ka iya rushewa matukar wadanda ake bai wa irin wannan rance, suka ci gaba da yin halin kaza da Hausawa ke cewa kin ci kin goge baki.











