Coronavirus: China za ta taimaka wa Najeriya da kasashen Afirka

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin China ta ce a shirye take ta taimaka wa Najeriya da sauran kasashen Afirka idan cutar Coronavirus mai shafar nimfashi ta bulla a nahiyar.
Jakadan kasar China a Najeriya, Zhou Pinjian ne ya sanar da haka yayin wata ganawa da manema labarai a ofishin jakadancin kasar da ke Abuja.
Ya bayyana cewa: "China na kokarin samar da mafita ga wannan annobar kuma ko bayan annobar ta shude, za ta ci gaba da duba hanyoyin da za ta taimaka wa kasashen Afirka domin mun dauki dangantakarmu da Afirka da muhimmanci.
"A fadin kasar ta China, mutum 17,205 ne aka tabbatar sun kamu da cutar kuma fiye da 17,200 a ke hasashen suna dauke da kwayar cutar ta coronavirus mai shafar numfashi, wadda kawo yanzu ba a sami maganinta ba ballantana rigakafi." in ji Pinjian.
Jakadan ya ce akwai 'yan China kusan mutum 40,000 zuwa 50,000 da ke zaune a Najeriya saboda dalilan kasuwanci kuma akasarinsu suna zaune ne a Legas da ke yankin Kudu maso Yammacin kasar.
A cewarsa, kimanin 'yan Najeriya 60 ne a yankin Wuhan - garin da annobar ta coronavirus ta bulla a kasar China.
Ya ce mafi yawan 'yan Najeriya sun fi zuwa birnin Guagzhou ne da ke Arewa maso Yammacin yankin Hong Kong.
Jakada Pinjian ya kuma nuna jimami kan irin asarar da kasar ta China da kasashen duniya ke fuskanta sakamakon annobar coronavirus.
Mutum na farko da ya mutu sakamakon cutar a wajen China ya rasu ne a kasar Philippines.
Tuni dai hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana cutar a matsayin babbar annoba a duniya.











