Za a bude sabon asibitin Coronavirus a China

@

Asalin hoton, Getty Images

China ta kammala gina wani babban asibiti cikin kwana biyar domin kula da masu dauke da kwayar cutar coronavirus.

Ranar Litinin ne kasar za ta bude asibitin Huoshenshan mai fadin murabba'in mita 14,000 da ta gina bayan bullar bakuwar cutar.

Hukumomin China sun ce asibitin Huoshenshan zai dauki gado 1,000.

@

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta ayyana coronavirus a matsayin babbar annoba a duniya. Mutum 14,000 sun kamu da ita kuma ta kashe mutum 304, inji gwamantin China. Ana zargin wasu mutun 100 a kasa 22 na dauke da kwayar cutar.

A ranar 24 ga watan Janairu ne China da tura manyan motoci da kayan aiki domin aikin gina asibitin.

@

Asalin hoton, Getty Images

Adadin wadanda suka kamu da coronavirus a duniya ya haura na annobar cutar Sars wadda kasa da mutum 30 suka kamu da ita a shekarar 2003. Mutum 8,000 ne suka kamu da kwayar cutar Sars a tsawon lokacin.

@

Asalin hoton, Getty Images

An fara samun cutar coronavirus ne a yankin Wuhan na kasar China mai yawan al'umma 11,000,000.

Gidan talabijin na gwamantin China ya ruwaito cewa sabon asibitin na Huoshenshan zai dauki gado 1,000 na kwantar da marasa lafiya.

@

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani ma'aikaci dauke da wani bangare na kayan gini
@

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Motocin gini da na hake-hake suna gyara filin da za a gina asibiti
@

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu injiniyoyi a lokacin da suke yin dabe a wurin ginin.

Gidan talabijin na CCTV ta rika yada wa duniya yadda aikin gina asibitin ke gudana kai tsaye domin jama'a su gani, kuma jama'a sun yi ta bibiyar tashar fiye da a kowane lokaci.

Mutum miliyan arba'in ne suka kalli yadda ake aikin gina asibitin kai tsaye ta talabijin a fadin China, inji jaridar Global Times.

@

Asalin hoton, Getty Images

@

Asalin hoton, Getty Images

Nuna ginin asibitocin kai tsaye ya sa jama'ar kasar kara ganin kimar motocin da ake aikin gine-gine da su.

Jama'ar kasar sun rika yi wa motar kwaba siminti kirari da sunan 'Sarkin Siminti' da 'Babban Farin Zomo' da sauransu.

"

Asalin hoton, Getty Images

An gina asibitin ne a wani bangare na asibitin Xiaotangshan da aka fara ginawa a birnin Beijin domin yakar cutar Sars a shekarar 2003.

@

Asalin hoton, Getty Images

An gina asibitin na Xiaotangshan ne a cikin kwana bakwai, abin da ake gani a matsayin ginin asibiti mafi sauri a duniya a wancan lokacin.

@

Asalin hoton, Getty Images

"China na da tarihin kammala abubuwa cikin harzari, ciki har da manyan gine-gine kamar wannan asibiti," inji Yanzhong Huang, wani babban jami'in lafiya a cibiyar hulda da jama'ar kasashen waje.

@

Asalin hoton, Getty Images

@

Asalin hoton, Getty Images

Asibitin Huoshenshan na dauke da wasu sassan gini da aka riga aka kera, kamar asibitin Xiaotangshan da ke Beijing din.

@

Asalin hoton, Getty Images

Mista Huang ya ce za a kawo injiniyoyi daga fadin kasar domin ganin an kammala a aikin kan kari.

"Aikin injiniya shi ne abin da China ta fi kwarewa a kai, Kasar na da tarihin gina dogayen benaye cikin sauri. Kasashen yammaci na mamakin hakan, amma tana yiwuwa,'' inji shi.

@

Asalin hoton, Getty Images

@

Asalin hoton, Getty Images