Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Burtaniya ta fice daga Tarayyar Turai
Burtaniya ta fice daga Taryyar Turai a hukumance bayan shekara 47 a kungiyar- kuma bayan shekara uku da yin zaben raba gardamar ficewar.
Wannan lokaci mai dumbin tarihi ya wakana ne a dai-dai karfe 11 agogon GMT kuma yayin da wasu ke murna da shagulgulan ficewar, wasu kuwa zanga-zangar kin amincewa suka gudanar a Burtaniyar.
Firayim minista Boris Johnson ya lashi takobin hada kan kasar da kuma ciyar da ita gaba.
Tun da misalin karfe hudu da rabi agogon GMT ne aka saukar da tutar Tarayyar Turan a ofisoshin wakilan Burtaniya da kuma sauran cibiyoyin EU a Brussels.
Ya ce duk da karfin ikonta, EU ta sauya a shekaru 50 da suka gabata kuma sauyin bai yi dai-dai da irin wanda Burtaniya ke muradi ba.
An gudanar da shagulgula a manyan shagunan sayar da barasa a fadin Burtaniya yayin da kasar ke kirga sa'o'inta na karshe kafin ficewar.
Daruruwan mutane sun taru a Dandalin Parliament don murnar ficewar, inda suke rera wakokin kishin kasa da tafa wa jawaban manyan shugabannin da suka jagoranci ficewar, ciki har da Nigel Farage.