Yaya 'yan Kaduna ke kallon salon mulkin Gwamna Malam Nasir El-Rufa'i?

Jihar Kaduna ce ta uku wurin yawan al'umma a Najeriya
Bayanan hoto, Jihar Kaduna ce ta uku wurin yawan al'umma a Najeriya
    • Marubuci, Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist

BBC ta gudanar da wani taron tattaunawa na ke-ke da ke-ke da gwamnan jihar Kaduna, inda al'ummar jihar suka samu damar yi masa tambaya kan alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe da kuma karbar mulki.

A lokacin da aka fara tattaunawar wadda aka yi wa lakabi da 'A Fada A Cika' a garin Kaduna, gwamnan ya ce ya dauki alkawura 81 a lokacin yakin neman zabe.

"Da muka fara neman shugabancin wannan jihar mun yi alkawura guda 81, kuma lokacin da za a sake wannan zaben na baya mun duba mun ga wane alkawarin ne muka cika, wanne ne muke kan cikawa, kuma wanne ne ba mu cika ba.

"Cikin alkawurra 81, biyar ne kawai wadanda tunda aka zabe mu muka kasa farawa."

A cikin alkawurran biyar da gwamnan ya ce gwamnatinsa ba ta cika ba akwai wasu muhimmai guda biyu:

  • Samar da gidaje 20,000 ga masu karamin karfi cikin shekara hudu.
  • Samar da jirgin kasa wanda zai rinka safara a Kaduna, babban birnin jihar.
Bayanan bidiyo, Shirin A Fada a Cika a Kaduna

A bangaren alkawuran da gwamnan ya cika kuwa akwai:

  • Sanya yaronsa makarantar gwamnati.
  • Bunkasa samar da kudaden shiga na cikin gida.
  • Aikin sabunta babban birnin jihar.
Wannan layi ne

Sai dai BBC ta ji ta bakin al'ummar jihar kan wasu daga cikin alkawuran da gwamnan ya yi a lokacin yakin neman zabe da kuma shan rantsuwar kama mulki.

Bangarorin da BBC ta duba sun hada da na kiwon lafiya, da ilimi, da tsaro, da walwala, da kuma bunkasa tattalin arziki.

Mutane kimanin 200 ne suka halarci taron tattaunawa da gwamna El-Rufa'i

Kiwon lafiya

A lokacin kama mulki a shekarar 2019, Malam Nasir El-Rufa'i ya yi alkawari kan kiwon lafiya.

Ya ce "Ina kara tunasar da iyaye mata cewar kiwon lafiya ga yara 'yan kasa da shekara biyar kyauta ne, don Allah ku ci gajiyar wannan tsari, ku rinka kai yaranku ana duba su lokaci zuwa lokaci, kyauta ne."

Sai dai a wani asibiti da BBC ta ziyarta, ta tattauna da wasu iyaye mata guda biyu, wadanda dukkaninsu aka kwantar da yaransu.

Sun shaida wa BBC cewa suna kashe kudade a duk lokacin da suka kai yaransu asibiti domin neman lafiya.

Wasu daga cikin mahalarta taron sun bai wa gwamnan shawarwari

Mace ta farko ta ce "Mun sayi dirif da magunguna, mun kashe kudi Naira 4,500, da kuma kudin gado, kuma har yanzu ana cewa mu sayi Sirinji, mu sayi wasu kananan abubuwa."

Mace ta biyu ta ce "Ina kashe Naira 3,000 ko 5,000. Tun da nake zuwa(asibiti) ba a taba ba ni(magani) kyauta ba sai wannan karon, shi ma ruwa ne kawai aka ba mu."

Haka nan kuma daya daga cikin mahalarta taron Najib Tsafe, ya bayyana cewa ba a aiwatar da tsarin bayar da maganin kyauta ga yara a asibitocin da yakan tura iyalinsa.

Ya ce "Alal hakika, idan ana kawo maka rahoton cewa ana bayar da magani kyauta, ko kuma ana duba kananan yara ko mata kyauta, to wannan ba haka yake ba."

"A duk lokacin da zan tura matata asibiti sai na ba ta kudin da za a sayi magani, hatta gwaji ma sai an yi."

Wannan layi ne

Tsaro

A wani jawabi da gwamnan ya yi sa'ilin kama mulkinsa karo na biyu a shekarar 2019, ya ce "Mun kashe makudan kudade wajen magance matsalar tsaro a cikin gida, mun sayi motoci da kayan aiki.

"Wadannan kudade zai fi kyau a karkata su wajen ci gaban yankunan da ake zaman lafiya."

Sai dai a lokacin taron da BBC ta gudanar, wani dan jarida da ya fito daga yankin Birnin Gwari, Zubairu Idris Abdbul-Rauf, ya ce a yankinsu mai fama da rashin tsaro, ba su ga motocin da gwamnatin jihar ta raba ba.

"Wadannan motoci da ka ce an raba ba mu ga ko daya ba a Birnin Gwari. Idan mutum zai bi hanyarmu sai dai ya bi da alwalarsa, idan (mutuwa)ta kasance gare ka, sai dai a turbude ka a wurin."

Bayanan bidiyo, Shirin A Fada a Cika a Kaduna

Haka nan kuma wani direba mai suna Nuhu, wanda ke safara tsakanin Birnin Gwari da Kaduna ya shaida wa BBC cewa "Lokacin da (Gwamna)ya zo kamfe ya ce mana ko hedikwatar tsaro ta kaduna za ta koma Birnin Gwari, sai ya tabbatar da tsaro a Birnin Gwari, to amma a halin yanzu babu tsaron sai tsoro".

"Saboda haka muna kira ga gwamna ya tuna da wannan alkawari da ya yi, ya dubi al'ummar Birnin Gwari da sauran al'ummar jihar Kaduna a kan abinda ya shafi tsaro."

Wasu sun koka kan lalacewar hanyoyi

Tsohon jami'in yada labarai na 'APC Akida' a jihar Kaduna Murtala Abubakar shi ma ya koka game da gazawar gwamnatin ta jihar Kaduna a bangaren tsaro.

Inda ya ce "Tunda ake a jihar Kaduna, ba a taba samun gwamnati wadda saboda sakaci da rashin iya tafiyar da mulki ta jefa jihar Kaduna a cikin rashin tsaro irin gwamnatin Nasir El-Rufa'i ba."

Sai dai a lokacin da ya mayar da martani game da rashin tsaro, gwamnan ya ce sabbin dabaru da masu aikata laifi ke bullo da su lokaci zuwa lokaci ne ya sanya ba a ganin tasirin kokarin da gwamnati ke yi wurin tabbatar da tsaro.

A bangare daya kuma gwamnan ya koka game da babban kalubalen da ya ce gwamnati na fuskanta a wurin yaki da masu aikata laifuka.

Jihar Kaduna ce ta uku wurin yawan al'umma a Najeriya
Bayanan hoto, Jihar Kaduna ce ta uku wurin yawan al'umma a Najeriya

Ya ce "A ganina, yau idan za a sa sojojin sama a cikin sati daya ko biyu, su bi dazuzzukan nan su rinka jefa wa wadannan 'yan ta'adda bama-bamai, sannan sojojin kasa da 'yan sanda su jira su(a gefen daji), duk wanda bam bai kashe shi ba idan ya fito a gama da shi, wallahi idan aka yi haka za a yi maganin wannan abu."

"To amma damuwar gwamnati ita ce masu kare hakkin bil'adama ne za su ce sojoji sun kashe farar hula."

"Su kansu sojoji suna jin tsoro saboda kada a ce sun kashe fararen hula, a ce International Criminal Court na neman ka."

Wannan layi ne

Tattalin arziki da sana'o'i

Aikin sabunta birnin Kaduna da gwamnatin jihar ta Kaduna ta bullo da shi ya zo da tangarda.

Duk da cewa an kirkiro shirin ne domin samar da tituna da kuma kawata babban birnin jihar, amma kananan 'yan kasuwa na kokawa kan korar su daga wurin sana'o'insu ba tare da an samar masu wani muhallin ba.

Hakan na faruwa ne duk da irin alkawarin da gwamnan jihar ya dauka na ganin ya tallafa wa al'umma wurin ganin sun tsaya da kafafuwansu

Yawancin mutanen da BBC ta zanta da su a garin Kaduna sun nuna rashin jin dadi game da wannan mataki.

Mata a wurin taron sun yi tambayoyi kan lafiya da ilimi

Wata karamar 'yar kasuwa mai suna Ruth Zubairu, wadda ta tattauna da BBC ta ce "Ka ba mu takardar tashi, dole mu bar nan(Shago) zuwa gobe, to ban san inda ka ke so mu koma ba, ta yaya kake so mu biya kudin makarantar yara?"

"Saboda kai kana cikin daula a gidan gwamnati, mu kuma, mu da ya kamata a ce kana kulawa da mu muna ta shan bakar wahala."

"Ni dai na san wannan ba daidai ba ne, ba na farin ciki kwata-kwata da wannan lamari."

Sai dai gwamnan ya ce yana daukar matakan rushewa da sake gina wuraren sana'o'i ne saboda a tabbatar da tsari a birnin na Kaduna.

Kuma a cewarsa 'yan kasuwar da aka tayar daga wuraren sana'o'insu za su samu shaguna bayan gwamnati ta gama aikin da take yi.

Bakman, wani dan kasuwa da aka rushe shagonsa

Walwala

Bayan hawa mulki a shekara ta 2015, gwamnan ya dauki matakin korar malaman makarantar firamare wadanda ake ganin ba su kware kan ayyukansu ba, kuma ya kori dubban ma'aikatan kananan hukumomi bayan wani tantancewa da aka gudanar.

BBC ta yi hira da wata tsohuwar shugabar makarantar firamare wadda ta ce ta shiga mummunan hali bayan da aka kore ta daga aiki ba tare da an biya ta hakkokinta ba.

Matar mai suna Perpetua ta ce "Abinda ya fi sosa min zuciya shi ne hatta ma kudaden da nake tarawa duk wata Naira dubu bibbiyu ba a ba ni ba."

Mahalarta shirin A Fada a cika

Wata tsohuwar ma'aikaciyar karamar hukuma da ta halarci taron, Hadiza Lere, ta ce da yawa daga cikin ma'aikatan da aka yi wa ritaya a lokacin mulkin gwamnan suna tsaka-mai-wuya saboda ba su samu hakkokinsu ba.

Wannan layi ne

Ra'ayoyi dai sun banbanta game da ko gwamnan ya taka rawar da ta dace wajen cika alkawurran da ya dauka ko kuma a'a.

Amma wani abu da ya bayyana a fili shi ne gwamnan ya zo da wani tsari na daban wurin gudanar da ayyukansa, wadanda suka sha banban da na gwamnonin da suka gabata.

Nuhu direba
Bayanan hoto, Al'ummar jihar Kaduna na da mabambanta ra'ayoyi kan salon mulkin gwamnan

BBC tare da hadin gwiwar gidauniyar MacArthur ne suka dauki nauyin wannan shiri.Wadanne alkawura El-Rufa’i ya fara cikawa?