Abubuwa 5 da Sarki Sanusi II ya fada da ya ziyarci Ganduje

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya yi kira ga al'ummar jihar da su bai wa shugabanni goyon baya domin su samu damar yi wa mutane ayyukan ci gaban da suka kamata.

A ranar Litinin ne Sarkin ya yi wannan jawabi a lokacin da ya raka Oba na Benin Omo N'Oba N'Edo Uku Akpolokpolo Ewuare II gidan gwamnatin jihar domin ganawa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, tare kuma da yi wa gwamnan murna.

Wannan ziyarar ta zo ne a ranar da sauran sarakunan jihar suka kai wa Gwamna Ganduje ziyara domin yi masa murna kan nasarar da ya samu a kotun koli.

BBC ta tattaro abubuwa biyar daga cikin kalaman sarkin a yayin ziyarar, wanda ta samu muryar tasa daga masarautar.

Taya murna

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya fara jawabin ne da taya Gwamna Abdullahi Umar Ganduje murnar samun nasararsa a Kotun Kolin kasar a makon da ya gabata.

Sarkin ya ce da yake wannan lokacin ne karo na farko da ya ziyarci fadar gwamnati tun bayan hukuncin kotun.

Ya ce ya ji dadi da ya samu damar zuwa da kansa don yin amfani da wannan damar ya yi murna, maimakon aiko da 'yan majalisar sarki kamar yadda da farko suka yi niyyar yi.

"Zan so na yi amfani da wannan damar a madadina da masarautata na yimaka murnar nasararka a Kotun Koli."

A lokacin da sarkin ya taya gwamna murna, wajen ya rude da tafi.

Hadin kai

Sarki Sanusi ya ce ya saurari jawabin gwamna bayan hukuncin kotun ya kuma ji shi yana kira ga al'umma da su hada kai.

"To ni ma ina son na kara muryata a kan wannan na yi kira ga jama'a su hada kai."

"Muna kira ga jama'a da su ji wannan kira na hadin kai su kuma bayar da hadin kan," in ji sarkin.

Yarda da hukuncin Allah

Ya kuma tabo batun yarda da duk wani hukunci da Allah ya zartar da bukatar mutane su rungumi hakan da hannu biyu.

"A matsayinmu na Musulmai mun san cewa mulki na Allah ne kuma yana bai wa wanda ya so a sanda ya so. Kuma idan ya ga dama ya bayar to akwai bukatar kowane Musulmi ya ajiye abin da ke ransa ya yarda da hukuncin Allah.

"Ya wajaba a kanmu mu yi wa shugabanninmu addu'a saboda idan suka yi da kyau suka kuma yi aiki nagari mutane ne za su mori hakan, sannan idan ba su yi abin da ya dace ba mutane ne za su wahala."

Bai wa gwamnati goyon baya

Sarkin ya sha alwashin cewa za su ci gaba da bai wa gwamnati goyon baya da hadin kai a kan duk wasu abubuwa da suka shafi walwala da ci gaban jama'a.

Sannan ya yi addu'ar "Allah ya ci gaba da bai wa jihar Kano zaman lafiya da cigaba."