Najeriya: Kasuwar Sabo Shagamu ta jihar Ogun ta kone

Kasuwar Sabo Shagamu da ke jhar Ogun a kudu maso yammacin Najeriya ta kone kurmus sakamakon gobarar da ta kama da tsakar daren Litinin.

Gobarar ta jawo hasarar dukiya ta miliyoyin naira amma ba a samu labarin salwantar rayuka ba.

Ya zuwa yanzu babu cikakken bayani game da musabbabin gobarar wacce ta tashi a lokacin da 'yan kasuwa ke gida.

Wasu 'yan kasuwar da gobarar ta kona rumfunansu a kasuwar ta Sabo Shagamu sun shaida wa BBC cewa sun yi asarar dukiya fiye duk yadda ake tunani.

Sakataren al'ummar arewacin Najeriya a garin Sagamu Alhaji Inuwa Sarki, ya shaida wa BBC cewa wasu daga cikin 'yan kasuwar sun yanke jiki sun fadi bayan samun labarin gobarar, yayin da wasunsu suka fito cikin tashin hankali.

Rahotanni sun ce 'yan kwana-kwana ba su samu zuwa kasuwar domin kashe gobarar da wuri ba, kuma ko da suka zo babu ruwa a motocinsu.

Sai da Jami'ar Babcock da kamfanin man fetur na NNPC ne suka taimaka da abin da suka iya wurin kashe gobarar.

Kasuwar Sabo Shagamu mai dadadden tarihi ta zama wata cibiyar hada-hadar sufurin goro a tsakanin jihohin arewacin Najeriya zuwa Jamhuriyar Nijar da Ghana da dai sauransu.

Kasuwanni a Najeriya na fuskantar iftila'in gobara da a wasu lokuta ake dangantawa da sakacin 'yan kasuwa masu barin wutar lantarki a kunne, ko kuma barin garwashin wuta da ba a kammala kashewa ba.

Sai dai wasu na zargin wasu 'yan kowa ya rasa da hannu a ciki.

Gwamnatin jihar Ogun ta je garin na Sabo Shagamu inda ta yi jaje tare da bayar da tabbacin yin bincike don gano abin da za ta iya yi ga wadanda suka yi asara.

Tashin gobara na daga cikin manyan kalubale da ke lakume dukiya a kasuwannin Najeriya, abin da a kan danganta da rashin kyakkyawan tsari.

Wannan ne ya sa wasu jihohin kudu maso yammacin kasar fara tayar da wasu kasuwanni suna gina na zamani domin samun kariya daga gobara.