Mutumin da ya maka Aung San Suu Kyi gaban kotun duniya

Asalin hoton, Getty Images
Matakin da Ministan shari'a na Gambia, Abubacarr Tambadou ya dauka ne ya sanya Aung San Suu Kyi gurfana gaban kotun duniya da ke Hague don musanta zargin da ake yi wa sojojin kasarta na yi wa musulmi marasa rinjaye na kabilar Rohingya kisan kiyashi.
Yayin da kotun kolin Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da umarnin dakile ci gaba da kashe-kashe, Anna Holligan ta yi nazari kan Aung San Suu Kyi matar da ta taba lashe lambar yabo ta zaman lafiya wato Nobel.
Ministan ya bayyana cewa "Na fahimci irin barnar da aka yi sabanin abin da muka gani kan akwatin talabijin," kamar yadda ya fada wa BBC.
"Sojoji da farar hula suna shirya hare-hare kan kabilar Rohingya tare da kona gidaje da kwace jarirai daga hannun iyayensu mata sannan su wulla su da ransu cikin wuta mai ci daga nan kuma su kashe maza da 'yan mata sannan kuma a yi musu fyade tare da cin zarafinsu."
Kabilar Rohingya, tsirarun musulmi ne da ke zaune a Myanmar da akasarin al'ummarta ke imani da addinin Bhudda.
'Kamar dai Rwanda'
Irin wadannan na tuna wa da Mista Tambadou irin abubuwan da suka faru a Rwanda lokacin kisan kare dangi a 1994 har ta kai ga kimanin mutum 800,000 sun mutu.
"Lamarin ya yi kusa da irin abubuwan da aka kaddamar kan kabilar Tutsi a Rwanda.
"An yi amfani da tsari iri daya - yadda aka kashe mutane ake kuma kiran su da sunaye - duk ya yi dai-dai da alamomin kisan kare dangi.
"Na sa a raina cewa wani yunkuri ne da hukumomin Myanmar suke yi na murkushe 'yan kabilar Rohingyan gaba daya."

Asalin hoton, AFP
Myanmar dai ta musanta zargin aikata laifin kisan kiyashi kuma a wannan makon ne aka fitar da "takaitaccen bayani" na wani bincike da gwamnati ta gudanar game da kisan mutane a matsayin "martani" da sojoji suka yi a kan hare-haren da mayaka masu kishin addinin Musulunci suka kai.
Bayanan da aka saki 'yan kwanaki kafin hukuncin kotun duniya ta ICJ, da alamu wani yunkuri ne na wanke hukumomi daga zargin.
A kotun, Aung San Suu Kyi ta ce binciken cikin gida da aka yi ya warware bukatar sa bakin kasashen duniya.
A wajen Mista Tambadou, zura ido ana kallon batun ba shi ne mafita ba.
"Batu ne da ya shafi jama'a," ya fadi hakan cikin yanayin daga murya.
"Na ji takaicin abin da na gani da wanda kuma na ji, a tunanina, ya kamata ace an tuhumi Myanmar bisa aikata wadannan laifuka kuma yin hakan shi ne a kai batun gaban kotun duniya ta ICJ."
Bayan da kotun ta ICJ ta goyi bayansa tare da bayar da umarnin hana kisan na kare dangi, Mr Tambadou ya shaida wa BBC cewa "ya gamsu matuka."
"Ina ganin hakan wata nasara ce ga dokokin kasashen duniya da kuma shari'ar duniya. Kuma kasashen duniyar ne - kamar yadda kotun ICJ ta wakilta - ke cewa ba za a lamunci kisan kare dangi ba."
Ga wannan tsohon mai gabatar da kara a kotun Majalisar Dinkin Duniya ta Rwanda da ya tsinci kansa a cikin sansanin 'yan gudun hijira a Bangladesh yana tunanin kaddara ce kawai."
An zargi Myanmar da aikata kisan kare dangi. Duk wata kasa cikin kasashe 149 da suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya, za ta iya shigar da kara, amma Gambia, a karkashin jagorancin Mr Tambadou ce ta dauki wannan matakin, wanda Kungiyar hadin kan kasashen Musulmai OIC mai kasashe mambobi 57 kuma mafi yawa kasashen musulmi ke goyon baya.

Gambia ta bukaci kotun ICJ da ta gaggauta yanke hukunci kan bukatarta ta matakan bayar da kariya wadanda aka tsara don hana duk wani tashin hankali da kuma kiyaye duk wata shaidar kisan kare dangi a kan musulmin Rohingya.
'Rashin tsoro'
Simon Adams, Shugaban kungiyar kare hakkin bil adama ta Global Centre for the Responsibility to Protect, ya ce mutum daya ne ya nuna jarumta da kwarewa wajen tuhumar Myanmar da zargin aikata laifukan kisan kare dangi.
"Wasu na tsoron ramuwar gayya daga 'yan China," a cewarsa.
"Wasu kuma na ganin lokacin bai yi dai-dai ba, yana da hadari a siyasance. Amma na ji dadin yadda ya nuna rashin tsoro. Ya san da irin matsin lambar da zai iya fuskanta amma ya bijiro da dabarar kawar da ita,"

Asalin hoton, Getty Images
Wannan rashin tsoro wani abu ne da ya kasance a rayuwar Mr Tambadou.
An haife shi a 1972, ya girma a babban birnin Banjul da ke Gambia kuma yana da 'yan uwa 18.
Maihaifinsa yana da mata uku. A matsayinsa na matashi, ya yi suna a harkar wasanni inda ya rika ciyo wa kasarsa kyaututtuka a fagen kwallon kafa. "
Yadda aka tuhumi manyan abokansa
Ya bayyana cewa ya samu sa'a a lokacin da yake tasowa. Iyayensa na iya biyan kudin makarantarsa har zuwa lokacin jami'a.
Ya ajiye burinsa na harkar wasanni domin gudun kada ya yi abin da mahaifinsa ba zai yi alfahari da shi ba inda ya zabi karatu.
"Ban taba sawa a raina zan karanci fannin shari'a ba amma jami'ar farko ta bani gurbin karanta fannin shari'a."
Bayan kammala jami'a, ya koma gida inda ya kasnace mai gabatar da kara na gwamnati.
Sanin irin yadda siyasa take a Gambia ya sa shi da abokanansa suka fara fitowa suna magana kan take hakkokin bil adama.
A Afrilun 2000, dakarun Shugaba Yahya Jammeh suka bude wa dandazon jama'a masu zanga-zanga wuta, tare da kashe dalibai 14 da dan jarida guda da kuma wani mai aikin sa-kai a kungiyar Red Cross.

Asalin hoton, AFP
Mr Tambadou ya kalli yadda aka tuhumi makusantansa amma matsin lamba ne daga danginsa saboda damuwar da suka yi da adawar da ya yi wa gwamnatin Jammeh wanda hakan ya sa ya bibiyi damarmakin da ke wajen mahaifarsa.
Daga nan kuma ya fara aikinsa a fannin shari'ar duniya.
Ficewar da ya yi da kansa don neman mafaka ta dauke shi zuwa kotun Majalisar Dinkin Duniya wadda aka kafa don ta yi kokarin gurfanar da wadanda suka haddasa kisan kare dangi a Rwanda, inda shi ke da alhakin gurfanar da tsohon shugaban sojojin Rwandan Manjo Janar Augustin Bizimungu.
Ya yi imani da abin da yake yi "ba wai kawai gabatar da masu hannu a kisan kare dangi ne na Ruwanda ba," in ji shi.
"Wannan wata hanya ce gare mu mu 'yan Afirka mu aika sako ga shugabanninmu ... Na ga hakan a matsayin gwagwarmayar Afirka ne ta neman adalci da nuna gaskiya fiye da na kasar Rwanda."
'Misali ga kasashe masu tasowa'
Bayan faduwar gwamnatin Jammeh a farkon shekarar 2017, Mr Tambadou ya koma Gambia domin yin aiki a majalisar zartarwar Shugaba Adama Barrow - sabon shugaba na farko da Gambia ta yi cikin shekara 23.
Kuma yana rike da mukamin ministan shari'a ne ya tafi New York tare da ministan harkokin wajen kasar, Ousainou Darboe.
Lokacin da Mr Darboe bai sami damar tafiya zuwa Bangladesh ba kamar yadda aka tsara, sai ya nemi Mr Tambadou ya tafi a madadinsa.
Ya leka kundin adana bayanansa ya ce: "Me zai hana?"

Asalin hoton, Getty Images
Amma aikin Mr Tambadou na gaba na iya zama kusa da gida.
Zanga-zanga ta barke a Banjul, babban birnin Gambia a makon da ya gabata inda magoya bayan tsohon Shugaba Jammeh ke neman ya koma gida daga neman mafakar da ya tafi a Equatorial Guinea.
Cikin wani sautin murya da aka nada, ana iya jiyo Mr Tambadou na cewa yana goyon bayan zanga-zangar.
Ministan shari'ar yana ganin ba lallai ba ne ya koma amma idan har ya koma ya ce za a damke Jammeh.
"Babu abin da zai faranta mani fiye da ganin tsohon Shugaba Jammeh ya fuskanci laifuffukan da ya aikata kan 'yan Gambia.
Babu wani abu da ya taba hada ni da shi. Na kalubalanci yadda ya rika aikata ba dai-dai ba tun ranar da ya karbi ragamar mulki."
Yanzu haka dai hukumomi sun fara tattaunawa game da wuri mafi dacewa don gabatar da tuhume-tuhumen aikata manyan laifuka kan Mr Jammeh.
Za ta iya yiwuwa shigar da shari'a a kasa ko zuwa kotun yanki ko kuma zuwa kotun duniya.
Mr Tambadou na ganin wannan ne lokacin da Gambia za ta koma kan matsayinta a duniya. Yana da buri game da kokarin ganin an kare hakkokin bil adama.
"Muna son yin jagoranci abin kwatantawa.
"Kasancewar shari'ar a gaban kotun ICJ na nufin Gambia na nuna wa duniya cewa ba lallai ne ka sami ikon soja ko karfin tattalin arziki don musanta zalunci ba, hujjoji da kuma adalci ne kawai ka iya kare kasa''.











