'Matan Najeriya ba su iya soyayya kamar Turawa ba'

Wani matashi mai shekara 26, Isa Suleiman Panshekara dan asalin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ya bayyana cewa a yanzu ba zai iya yin soyayya da wata 'yar Najeriya ba bayan da ya hadu da masoyiyarsa Janine Sanchez mai shekara 46 a duniya.

A baya-bayannan ne dai labarin Isa da masoyiyar tasa Ba'amurkiya ya baza shafukan sada zumunta inda wasu da dama ke tsokaci game da masoyan wadanda suke ci gaba da tsinkar furen so.

Ita dai Janine ta niki gari tun daga Amurka zuwa Najeriya domin haduwa da matashin masoyin nata wanda ta aminta da shi.

A wata hira da Isa ya yi da BBC ya ce: "A gaskiya matanmu ba su iya soyayya ba, ko dai za ka ga suna da wata bukata ko kuma suna da buri amma idan baturiya ta ce tana sonka, toh tana fadin haka ne daga zuciyarta."

Isa wanda tsohon mai aski ne ya ce ya dan yi fargaba a lokacin da hukumar Hisbah da DSS suka gayyace su zuwa ofishinsu, sai dai ya ce sun ba su shawara ne game da yadda labarin nasu yake ci gaba da daukar hankali musamman a shafukan sada zumunta.

Masoyan dai sun fara haduwa ne ta shafin Instagram a shekarar da ta gabata.

"Mun fara ne bayan da na nuna sha'awar kasancewa daga cikin masu bibiyarta a shafin Instagram sannan idan ta wallafa hoto a shafinta ina danna alamar so wato liking."

"Bayan wani dan lokaci sai na lura akwai wasu 'yan damfara ta intanet da suke kokarin damfararta, sai na ankarar da ita kuma hakan da na yi ya burgeta har take cewa ni mutum ne mai gaskiya. Abin da na yi shi ne ya janyo hankalinta gare ni. "

"Daga nan muka fara aika wa juna sakonni har da kiran bidiyo kuma hakan ne ya kai mu ga inda muke a yanzu."

Isa ya ce iyayensa sun amince ya auri masoyiyar tasa Janine kuma nan da watan Maris za a yi bikinsu inda za su wuce Amurka.

"Bayan bikinmu a watan Maris idan Allah ya yarda, Amurka za mu wuce inda nake fatan samun aiki na koma makaranta sannan samu kungiyar da zan rika buga wa kwallo."

Ita ma Janine ta bayyana cewa wannan ne karonta na farko da ta ziyarci Afirka kuma ta nuna jin dadi kan yadda jama'a suka tarbeta.

Ta ce ta yi murna kwarai bisa yadda iyayen Isa suka amince su yi aure.

"Na gana da 'yan uwansa sama da mutum 100 kuma abin ya faranta mun rai kan yadda suka nuna goyon bayansu a garemu, akasarinsu ba su taba ganin Baturiya ba, haka suka rika wasa da gashina suna taba hannuna. "

Janine wadda kwararriyar mai girke-girke ce a wani shagon abinci na 'yan Afghanistan da ke Californina, ta ce za ta koma Amurka a watan Fabrairu kafin ta dawo gabanin bikinsu a watan Maris.

"Zan koma Amurka cikin wata mai zuwa kuma zan dawo a watan Maris domin bikinmu kafin daga bisani mu tafi zuwa Amurka."

A karshe Isa ya ce soyayyarsu da Janine tabbaci ne cewa mutum na iya gamo da katar da masoyinsa ta shafin sada zumunta kuma yana da kyau kowa ya gwada sa'arsa.