Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matashiya ta cinna wa kanta wuta a Zamfara saboda soyayya
Wata matsashiya mai suna Aisha Aminu mazauniyar Albarkawa a jihar Zamfara wadda ta cinna wa kanta wuta saboda an hana ta auren saurayin da take kauna ta rasu.
Aisha ta rasu ne a ranar Laraba bayan fama da jinya ta fiye da wata guda sakamakon raunukan da ta samu bayan cinna wa kan nata wuta.
Wani makwabcin su marigayiyar, ya shaida wa BBC cewa "yanzun nan muka dawo daga jana'izarta. Ta rasu ne tun karfe goma na safe."
Ya kara da cewa "saurayin marayiyar ya dimauce domin da kyar a ka dora shi a mota domin ya koma gida."
Kafin rasuwarta, Aisha ta shaida wa BBC cewa ta dauki wannan mataki ne saboda ba za ta iya hakura da shi ba kuma "da ta yi karuwanci gara ta kashe kanta" kawai.
Mahaifin Aisha Aminu Muhammad Albarkarawa ya shaida wa BBC cewa saurayi ne take so tsawon shekara daya amma Allah bai sa yana da abin aurenta ba.
"Saboda haka ne muka dakatar da shi da zuwa wurinta tunda ba shi da abin aurenta har sai Allah ya kawo mata wani.," in ji Aminu Muhammad.
Ya kara da cewa: "Ashe ita kuma tana sonsa sosai. Shi ne ta dauki wannan mataki ba tare da saninnmu ba, kawai sai ganinta muka yi tana ci da wuta, jama'a suka yti kokarin wutar.
"Da aka tambaye ta dalili sai ta ce ita wallahi tana sonsa ne kuma da ta je ta yi iskanci gara ta kashe kanta tun da ba shi da halin da zai iya aurenta."
Ita ma Aisha ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda tana sonsa kuma shi ma yana sonta.
Ta ce: "Na dauki wannan mataki ne saboda ina sonsa kuma tun da muke tare da shi bai taba gaya mani wata magana ba.
"Acaba (okada) yake yi saboda haka sai ya yi zaton cewa ba shi da wani hali. Ni kuma na ce da in je in yi karuwanci gara na kashe kaina na huta kawai. Sai na sa ma kaina fetur kawai, na sa ashana."
Aisha ta ce ta ji raunuka a hannayenta da bayanta da kuma ciki, sannan kuma ta ce ta yi nadama.
Sai dai ta ce ba ta san halin da masoyin nata yake ciki ba a halin yanzu domin har yanzu bai je dubiya ba.