Kotun Koli ta yi watsi da karar Abba Gida-Gida na Kano

Abba Kabir Yusuf
Bayanan hoto, Hukuncin na nufin Abba Kabir Yusuf na PDP ya kure damar da yake da ita ta daukaka kara

Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi da karar dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, tare da tabbatar wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kujerar.

Wata tawaga ta alkalan Kotun ce a karkashin jagorancin Mai Shari'a Sylvester Ngwuta yanke hukuncin ranar Litinin.

Sauran alkalan sun hada da Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun da Mai Shari'a Olukayode Ariwoola da Mai Shari'a Amina Augie da kuma Mai Shari'a Uwani Abba-Aji.

Wannan hukunci na Kotun Koli na nufin Abba Gida-Gida, kamar yadda aka fi saninsa, ba zai iya kara daukaka karar ba.

A ranar 12 ga watan Afrilun 2019 ne, Abba ya fara kai koke a gaban kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a titin Miller a babban birnin jihar ta Kano.

A wancan lokacin ya shaida wa BBC cewa sun je kotun ne domin su gabatar da dukkan takardunsu na korafe-korafe da lauyoyinsu suka tsara a kan zabukan da suka gudana na gwamna.

Dan takarar gwamnan ya ce a zaben da aka yi ranar 9 ga watan Maris na 2019, Hukumar Zabe ta Kasa a jihar ta sanar da sakamakon inda ta bayyana cewa jam'iyyar PDP ce ke kan gaba.

To amma daga bisani hukumar ta ce zaben bai kammala ba, inda aka sake yin wani a ranar 23 ga watan na Maris aka kuma bayyana dan takarar jam'iyyar APC, wato Gwamna Ganduje a matsayin wanda ya yi nasara, "bayan kuma kowa ya san duk abubuwan da suka faru a yayin zaben," in ji Abba.

Sai dai kotun sauraron kararrakin zaben ta yi watsi da karar tasa.

Kotun daukaka kara

Daga bisani ya kai karar gaban Kotun Daukaka Kara, wadda ita ma, a watan Nuwamban 2019, ta yi watsi da karar da jam'iyyar PDP ta shigar gabanta.

Kotun ta yi watsi ne da ikirari 24 da Abba Kabir da kuma PDP suka gabatar mata.

Me ya faru tun farko?

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano

Asalin hoton, Kano Government

Bayanan hoto, Kotun Kolin ta tabbatar wa Ganduje kujera don yin wa'adi na biyu

Abba Yusuf ya sha kaye a hannun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a karashen zaben da aka yi, duk da cewa shi ne kan gaba a zaben farko wanda bai kammala ba.

Ganduje ya ci zaben ne na biyu da tazarar kuri'a 35,637 inda jam'iyyarsa ta APC ta samu kuri'a 45,876 yayin da PDP ta samu 10,239.

Idan aka hada sakamakon zaben na farko da na biyu, jimilla APC ta samu kuri'a 1,033,695, yayin da PDP ta samu jimilla 1,024,713. Hakan na nufin Ganduje ya ci zaben ne da tazarar kuri'a 8,982.

Sai dai masu sa ido na gida da waje sun soki yadda aka gudanar da zaben na biyu, suna masu cewa an tafka magudi, zargin da jam'iyyar APC da kuma Hukumar Zabe suka musanta.