Tsohon Fafaroma ya ja kunne kan sauya dokar aure a cocin Katolika

Asalin hoton, Reuters
Fafaroma Benedict XVI mai murabus ya fitar da wata sanarwar kare kai kan batun dokar kin yin auren Fafaromomi a Cocin Katolika, yayin da magajinsa ke duba yiwuwar sassauta haramcin aure ga manyan malaman coci.
Fafaroma Benedict ya yi wannan kira ne a wani littafi da ya wallafa tare da wani babban malamin coci Cardinal Robert Sarah.
Wannan na zuwa ne a matsayin martani ga wani bayani da ke cewa za a bai wa maza masu aure damar zama manyan malaman coci a yankin Amazon.
Fafaroma Benedict, wanda ya yi ritaya a 2013 ya ce ba zai iya kauda kai daga lamarin ba.
A littafin, Fafaroma Benedict ya ce kaurace wa aure ko jima'i al'adar coci ce ta shekara da shekaru kuma tana da matukar muhimmanci saboda tana bai wa malaman damar mayar da hankali kan ayyukansu na coci.
Mai shekara 92 ya ce: "Ba zai yiwu a hada abubuwan biyu (limancin coci da aure) ba a lokaci guda".
Fafaroma Benedict, wanda shi ne shugaban cocin na farko da ya fara yin murabus cikin kusan shekara 600, bai cika saka baki a al'amuran cocin ba.
Har yanzu dai fadar Vatican ba ta ce komai ba kan littafin.

Asalin hoton, Getty Images











