A cikin hotuna: Yadda aka yi bikin kirsimeti a duniya
A Australiya da Amurka, an gudanar da addu'o'i a daya daga cikin ranaku mafi muhimmanci ga mabiya addinin kirista.
Ga wasu daga cikin kyawawan hotunan da aka dauko daga sassa daban-daban na duniya.
Colombo, Sri Lanka

Asalin hoton, EPA
Yara mabiya darikar Katolika sanye da tufafi da fuka-fukai mai nuna alamar kwaikwayar mala'iku, a Majami'ar St Anthony.
Tana daya daga cikin majami'u uku da 'yan kunar bakin wake suka kai wa hari a daren bikin Ista, inda mutum 54 suka mutu nan take, sama da 300 kuma suka mutu a sauran sassan kasar.
Abu Dhabi, Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa

Asalin hoton, EPA
Matashiya na kunna kyandir a Majami'ar St. Joseph"s Cathedral Catholic, da ke birnin Abu Dhabi na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, inda kasar ke da mabiya addinin Kirista da suka kai kashi 5 cikin 100.
Hanoi, Vietnam

Asalin hoton, AFP
Wannan matar na daukar hoton dauki da kanka a wajen Majami'ar Cathedral a birnin Hanoi na kasar Vietnam a ranar 24 ga watan Disamba 2019
Paris, Faransa

Asalin hoton, EPA
Bishop Philippe Marsset shi ne ya jagoranci addu'ar tsakar dare a Majami'ar Saint Germain l'Auxerrois.
A karon farko cikin sama da shekaru 200, an yi addu'o'in kirsimeti ba a cikin majami'ar Notre-Dame cathedral ba wadda ibtila'in gobara ya fada mata a watan Afirilu.
Nairobi, Kenya

Asalin hoton, Reuters
A daren kirsimeti, mabiya sun taru a Majami'ar Fort Jesus da ke birnin Nairobi na kasar Kenya, ranar 25 ga watan Disamba 2019.
Bethlehem, a yankin Falasdinu

Asalin hoton, EPA
An gudanar da addu'o'i a daren kirsimeti a Yammacin Kogin Jordan, garin da littafin Injila ya ce a can aka haifi Annabi Isa AS.
Birnin Vatican

Asalin hoton, AFP
Wannan shi ne karo na bakwai da Fafaroma Francis ke jagorantar addu'o'in kirsimeti.
A sakonsa na wannan rana Fafaroma ya ce ''Ubangiji yana kaunar kowa ciki har da mafiya aikata munanan zunubai,'' sakon dai mabiya addinin Kirista na kallonsa a matsayin shagube ga dambarwar da ta mamaye Fadar Vatican.
Sydney, Australiya

Asalin hoton, EPA
Sa'o'i gabannin bikin kirsimeti, aka yi zanen suka ga Firai Minista Scott Morrison sanye da riga mai budadden gaba da furanni, a daidai lokacin da kasar ta yi fama da wutar daji mafi muni a tarihi.
Dukkan hotuna suna da hakkin mallaka











