Tottenham ba za ta iya wasa ba Kane ba - Mourinho

Kocin Tottenham Jose Mourinho ya ce babu wani dan wasa da zai iya maye gurbin Harry Kane wanda a yanzu yake jinya kuma a cewarsa Tottenham ba za ta iya taka leda kamar yadda ta saba ba tun da baya nan.

Ya ce dan wasan wanda ya gurde a kafarsa yana bukatar a yi masa tiyata kuma ba zai buga wasa ba har zuwa Afrilu.

Kyaftin din Ingila Kane ya zura wa kungiyarsa kwallo 27 a kakar wasa ta bana cikin wasa 31 da ya buga mata.

Mourinho ya bayyana cewa "idan na cika magana kan Harry sai a ce ina da rauni. Gwara kawai na yi magana kan abubuwan da za su sani dariya."

Tottenham za ta karbi bakuncin zakarun gasar firimiya Liverpool ranar Asabar da karfe 17:30 agogon GMT.

Kane ya samu rauni a kafarsa a wasan da Tottenham ta sha kashi a hannun Southampton ranar daya ga watan Janairu kuma ba zai koma fili ba sai zuwa Afrilu.