EFCC ta je bincike gidajen Shehu Sani a Abuja

Asalin hoton, @ShehuSani
Jami'an hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa EFCC sun je bincike gidajen Sanata Shehu Sani a Abuja, ranar Laraba.
Shehu Sani wanda tsohon sanata ne mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya ya shafe kimanin kwanaki tara a tsare inda hukumar ke zarginsa da karbar ''kudade da sunan mukaddashin hukumar EFCC Ibrahim Magu''.
Suleiman Ahmed wanda wani mai taimaka wa Sanatan ne ya shaida wa BBC cewa jami'an sun shafe kimanin awa daya suna bincike a layin Negro Crescent da ke Unguwar Maitama Abuja.
Haka zalika ya shaida mana cewa jami'an sun shafe kimanin awa daya da mintuna talatin suna bincike a gidansa da ke layin Casablanca da ke Unguwar Wuse II da ke Abuja kuma sun yi awon gaba da katuna na adreshi wadanda aka fi sani da ''complementary cards''.
Bayan haka jami'an sun je ofishinsa da ke layin Monrovia a Unguwar Wuse II inda a nan ma sun gudanar da bincike.
Suleiman ya kuma tabbatar da cewa har yanzu Sanata Sani yana hannun hukumar ta EFCC.
Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren ya shaida cewa ba da dadewa zai fitar da sanarwa dangane da binciken da suka yi.
Tun a ranar biyu ga watan Janairu hukumar ta EFCC ta samu amincewa daga kotu kan tsare sanatan kan zarge-zargen da take yi masa.











