'Yan bindiga sun sace sama da mutum 30 a Katsina

Rahotanni na cewa wasu masu garkuwa da jama'a sun yi awon gaba da fasinjoji kimanin 30 a karamar hukumar Batsari a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Wata majiya ta ce masu garkuwar dauke da muggan makamai sun kai harin da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Lahadi inda suka yi awon gaba da mutanen da ke kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar Jibiya, mai makwabtaka.

Masu garkuwar dai sun tare mutanen ne a cikin motoci guda biyu.

Dan majalisar dokokin jihar Katsina, mai wakiltar karamar hukumar ta Batsari, Alhaji Yusuf Jabir ya tabbatar wa da BBC faruwar al'amarin.

Batun satar jama'a domin neman kudin fansa dai na kara kamari a jihar Katsina da ma wasu jihohi a Najeriya.

Ko a makon da ya gabata sai da masu garkuwar suka shiga har cikin gidan wata amarya suka yi awon gaba da ita a karamar hukumar Dutsen Ma.

Jihar Katsina na cikin jihohin da suka cimma sulhu da `yan bindiga, amma harin da ake kaiwa a baya-bayan nan na nuna cewa sulhun na fuskantar barazana.

Tun lokacin da gwamnatocin jihohin Katsina da Zamfara ke maganar sulhu da `yan bindiga, wasu masu sharhi a kan harkokin tsaro sun yi gargadin cewa wasu `yan bindigar za su iya mai da shirin wata hanyar tatsar gwamnati.