Nancy Pelosi ta ce tsokana ce kisan da Trump ya sa aka yi wa kwamandan Iran

Shugabar Majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta yi kakkausar suka a kan matakin gwmnatin Trump na takaita gabatar da takardar sanar da majalisar dokokin Amurkar, game harin jirgi maras matuki da ya hallaka Janar Qassem Soleimani na Iran.

Ms Pelosi, ta ce abu ne da ba a saba gani ba matuka a ce an boye takardar cikin sirri, sai kawai wasu 'yan kadan daga cikin shugabannin majalisa ne kawai aka aika wa.

Shugabar ta ce an bar Majalisar da alummar Amurka cikin duhu a kan abin da ya faru, wanda Shugaba Trump ya bayar da umarnin kai harin da ya hallaka Janar din ranar Juma'a.

Ta kira kisan Janar Soleimani tsokana, tare da kiran da a yi wa majalisar dokoki cikakkn bayani a kai.

Ita dai fadar gwamnatin Amurkar, White House, a hukumance ta sanar da majalisar dokokin kasar game da harin jirgi maras matukin da kai ta hallaka Janar Soleimani ranar Juma'a, wanda hakan ya kamata bisa doka gwamnatin ta yi cikin sa'a 48 da sanya dakarun Amurka cikin wani yaki ko rikici da makami.

Trump ya gargadi Iran kan ramuwar gayya:

Shugaban ya gargadi Iran da cewa Amurka ta ware wasu wurare har 52 na Iran da za ta kai wa hari, muddan Tehran ta kai hari kan duk wani Ba'amurke ko wata kadara ta Amurkar, domin ramuwar gayyar kisan k Janar Soleimani.

Shugaban, ya ce wuraren na a matsayin, Amurkawa 52 da aka yi gargkuwa da su a Tehran a 1979. kuma ya ce za a kai harin ne kan wuraren da ita kanta Iran cikin gaggawa kuma da karfin gaske.

Jana'izar Janar Soleimani:

Gawar Janar Qasem Soleimani, ta isa Iran, kafin a yi masa sutura ranar Talata.

An kai gawar ne birnin Ahvaz da ke kudu maso yammacin kasar, inda dubban masu makoki sanye da bakaken kaya suka taru domin alhini.

Gaba za a tafi da gawar birni mai tsarki na 'yan Shi'a, Mashhad, kafin daga bisani a tafi da ita mahaifarsa, garin Kerman da ke kudu maso gabashin kasar ta Iran, inda za a binne mamacin.

Kafin kai gawar Iran sai da aka kai ta biranen Iraqi masu tsarki na Najaf da Kerbala, amma tun da farko a Bagadaza, dubban mutane ne suka halarci jana'izar Janar din da kuma Kwamandan kungiyar sojin sa-kai ta 'yan Shi'a a Iraqi, Abu Mahdi al Muhandis, wanda Amurka ta kashe su tare.

Masu makokin wasunsu sanye da kayan soji na yaki sun rika tsine wa Amurka da kawayenta, tare da yin kira da a dau fansa.

.