Hatsarin jirgin sama ya ragu da kashi 50 cikin dari a 2019

Boeing 737 Max Planes Sit Idle As Company Continues To Work On Software Glitch.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutum 257 ne suka mutu a 2019 sabanin 534 a 2018

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin jirgin sama ya ragu da sama da kashi 50% cikin 100 a 2019, kamar yadda wani bincike da aka gudanar kan masana'antar sufuri ya bayyana.

A shekarar da ta gabata, mutum 257 ne suka mutu sabanin 534 a shekarar 2018, a cewar wani kamfanin sufuri To70.

An fitar da kididdigar duk da yawan hatsarin da jirgin Boeing 737 Max ya yi a Habasha a Maris din 2019.

Raguwar ta biyo bayan raguwar hadura da jiragen sama ke yi duk da samun karuwar tafiye-tafiye.

A 2019, an yi hatsari sau 86 da suka hada da jiragen fasinja har da hatsari takwas da aka yi, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutum 257, a cewar kamfanin sufurin na kasar Netherlands.

Mutum 157 da suka mutu a hadarin jirgin Ethiopian Airlines 302 a watan Maris su ne fiye da rabin adadin mutanen da suka mutu a 2019.

An yi tafiye-tafiye a jirgin fasinja sama da miliyan biyar a cewar rahoton.

Shekarar da ta gabata ita ce "daya daga cikin shekarun da ba a samu hatsarin jiragen fasinja ba" a cewar wani shafin da ke bibiyar hatsarin da jiragen sama ke yi, Aviation Safety Network.

A 2018, an samu hatsari 160 har da wasu hatsari 13 da suka yi sanadiyyar mutuwar mutum 534.

Rahoton ya nuna cewa 2017 ce shekarar da ba a fuskanci hatsaarin jirgin sama ba sannan hatsari biyu kawai aka samu a shekarar da suka halaka mutum 13.

Binciken ya hada da fasinjoji da masu aikin jirgin.

Ire-iren jiragen da binciken ya yi nazari a kansu su ne jiragen da mafi yawan fasinjoji suka fi tafiye-tafiye a ciki a fadin duniya.

Binciken bai hada da matsakaita da kananan jirage ba.

A watan Oktoban 2018 jirgin Boeing 737 Max na kamfanin Lion Air ya yi hatsari ya kuma hallaka mutum 189 da ke cikinsa.
Bayanan hoto, A watan Oktoban 2018 jirgin Boeing 737 Max na kamfanin Lion Air ya yi hatsari ya kuma hallaka mutum 189 da ke cikinsa.

Kazalika, rahoton bai kunshi hatsarin da suka shafi jiragen sojoji ba da na bayar da horo da jiragen 'kashin-kai da jiragen dakon kaya da kuma jirage masu saukar ungulu.

A shekarar 2019 ne aka tsananta bincike kan batun bai wa fasinjojin jiragen sama kariya bayan hatsari biyu da aka samu na jirgi kirar Boeing 737 Max.

A watan Oktoban 2018, wani jirgin Boeing 737 Max na kamfanin Lion Air ya yi hatsari ya kuma hallaka mutum 189 da ke cikinsa.

Wata biyar bayan haka kuma, wani jirgin Ethiopian Airlines ya yi hatsari ya hallaka mutum 157, abin da ya sa aka dakatar da tafiye-tafiye da jirgin na 737 Max.