Aisha Buhari: An yi wa Aisha ca don ta kira Buhari 'Janar'

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da matarsa Aisha Muhammadu Buhari

Asalin hoton, @aishambuhari

Bayanan hoto, Buhari ne da kansa ya ce ya fi son a kira shi da PMB, ba GMB ba
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja Bureau
  • Lokacin karatu: Minti 3

'Yan Najeriya sun sako Mai Dakin Shugaban Najeriya a gaba sakamakon kiran shugaban da "mai gaskiya" da kuma inkiyarsa ta "GMB" (General Muhammadu Buhari) maimakon "PMB" wato President Muhammadu Buhari a wani sakon Twitter.

Aisha Buhari ta wallafa sakon ne a shafinta na Twitter domin taya mijinta murnar cika shekara 77 da haihuwa a ranar Talata.

"Barka da murnar ranar haihuwa GMB nawa mai gaskiya," kamar yadda Aisha ta wallafa.

"Ina yi maka fatan Allah ya kare ka, ya kara maka lafiya domin ci gaba da jagorantar kasarmu. Allah ya bar mana kai GMB. Allah ya taimaki Najeriya!"

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Kamar dai Aisha ba ta san mai zai biyo baya ba a lokacin da ta wallafa sakon, amma wane ne zai zargi wani abu kawai don mata ta yi wa mijinta fatan alheri sannan ta kira shi da sunan da ta ga ya dace?

Su dai 'yan Najeriya ba a bar su a abaya ba kamar yadda suka saba, kuma Haidar Aliyu (@Haidar_Michika) ya ce: "Tun da Mama ma ta kira shi da GMB wane ne ni da zan kira shi da PMB!"

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Shi kuwa Martin's Izonowei (@SIzonowei) cewa ya yi "idan da gaske mai gaskiya ne to sai ya gina mana asibitoci masu kyau, ko kuwa wannan ba ya cikin abubuwa bakwai?"

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Shi kuma Albadoh (@MAlbadoh) ya ce ne "ai sunansa ne duka kuma ya cancanci sunayen".

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Wani mai suna Blessed Beyond Measure (BBM) @Drmuzoic cewa ya yi "ina fatan za ki samu damar tattaunawa da 'mai gaskiyar naki' GMB a daki".

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 5

GMB ko PMB?

Kasancewarsa tsohon shugaban mulkin sojin kasar, gabanin hawansa karagar mulkin farar hula a shekarar 2015, Buhari ya zabi yi wa kansa inkiya da GMB (General Muhammadu Buhari).

Daga baya ma ya ce zai rika manna "GMB" a jikin duk abin da ya wallafa a shafukan sada zumunta.

Bayan hawansa kan mulki ne kuma ya ce ya fi son a rika kiransa da PMB wato (President Muhammadu Buhari) maimakon GMB saboda yanzu shi mai shugabanci ne a tsarin dimokuradiyya, ba soja ba.

Sai dai kuma a makon da ya gabata ne jaridar The Punch ta ce za ta ci gaba da kiran Shugaba Buhari da inkiyarsa ta da wato Janar Buhari maimakon Shugaba Buhari.

Punch ta ce ta dauki wannan mataki ne "saboda take hakkin dan Adam da gwamnatin Buhari take yi musamman ci gaba da tsare Omoyele Sowore da hukumar DSS take yi" kuma ta kwatanta mulkinsa na yanzu da na mulkin soja.

"Shugaba Buhari" aka ci gaba da kiransa musamman a kafafen yada labarai kafin Punch ta dauki waccen mataki.

Kwatsam a ranar Talata kuma sai ga shi Mai Dakin Shugaban ta fito fili ta kira shi da GMB, abin da ya jawo martani iri-iri daga 'yan Najeriyar.

Wani mai suna Young_Journalist (@Abubakar_Mhmmad) ya ce: "General Muhammad Buhari😂😂😂 ni ma na dana".

Kauce wa X, 6
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 6

Shi kuwa Uche Samuel (@uchesame) cewa ya yi "lallai kuwa mai gaskiya".

Kauce wa X, 7
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 7

General Ola Azeez. (@Azeezsaka14) ya ce "Murnar ranar haihuwa, mun gode wa Allah, Mama ma ta bi".

Kauce wa X, 8
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 8