'Mazan da aka haifa ƙanana na iya fuskantar rashin haihuwa'

Asalin hoton, Getty Images
Jarirai maza da aka haifa kasa da kilogram uku, na da yiwuwar samun matsalar rashin haihuwa idan suka girma, in ji wani binciken kasar Denmark.
A farkon shekarunsu na 30, kaso 8.3 cikin dari na mazan da aka haifa 'yan kanana na da matsalar rashin haihuwa, idan aka kwatanta da kaso 5.7 cikin dari na wadanda aka haifa da nauyi dai-dai gwargwado.
Masu binciken sun ce rashin girma a ciki na iya janyo rashin ginuwar kwayoyin halittar maniyyi da ma sauran abubuwan da ke jiki.
Kusan kashi 12.5 cikin dari na ma'aurata na fama da matsalar rashin haihuwa.
Binciken ya gano cewa rashin haihuwa a mata ba shi da alaka da girmansu a lokacin da aka haife su.
Masana kimiyya a jami'ar Aarhus, sun duba sama da maza 5,500 da mata 5,300 tsakanin shekarun 1984 da 1987, sannan suka bi rayuwarsu har suka girma har zuwa shekarar 2017.
Cikinsu, kashi 10 cikin dari na maza da mata an haife su kanana; kashi 80 cikin dari kuwa an haife su dai-dai wa daida kuma kusan kashi 9 cikin dari an haife su da girma sosai.
Jariran da aka haifa a mako 40 suna da nauyin kilogram 2.5 zuwa kilogram 4.5 a wannan binciken.
Iyaye mata na jariran da aka haife su kanana masu shan taba da giya ne kuma bincike ya nuna cewa shan taba na taba lafiyar jarirai.
Manyan cutuka biyu, daya da ta shafi mafitsara daya kuma ta shafi 'yan maraina, na cikin abubuwan da suka fi jawo rashin haihuwa a maza.

Asalin hoton, Getty Images
Hanyoyin da za a bi don gujewa haihuwar karamin jariri
- A daina ko kuma a rage shan taba
- A daina shan miyagun kwayoyi
- A ci abinci mai kyau mai gina jiki kuma a rika motsa jiki
Mata na haihuwar jarirai kanana idan sun haura shekara 40 ko kuma idan suna da hawan jini ko ciwon koda ko ciwon suga.
Haka kuma, wani lokaci, jarirai ba sa girma yadda ya kamata saboda wasu dalilai kamar:
- Mahaifa ba ta aiki yadda ya kamata
- Kamuwa da wata cuta a ciki
- Idan jaririn ba shi da cikakkiyar halitta











