An yanke wa 'masu tsaurin kishin addini bakwai' hukuncin kisa

An yanke wa wasu masu tsaurin kishin addini su bakwai hukuncin kisa kan wani hari da suka kai kantin shan shayi a babban birnin Bangladesh, da ya yi sanadin mutuwar mutum 22 wadanda yawancinsu baki ne 'yan kasashen waje.

Wani gungun mutum biyar ne suka kai harin kantin shan shayi na Holey Artisan a Dhaka, inda suka yi garkuwa da mutanen da ke cikin kantin.

Mutum takwas aka yi wa shari'a, wadanda ake zargin su da shirya tare da samar wa maharan makamai. Amma an wanke mutum daya daga laifin.

Harin, wanda ya dauki tsawon sa'a 12 na garkuwa da mutanen, shi ne mafi muni da aka taba kai wa a Bangladesh. Yawancin wadanda abin ya rutsa da su 'yan Italiya da Japan ne.

Kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin, amma Bangladesh ta karyata hakan, a maimakon haka sai ta dora alhakin a kan wata kungiyar masu tayar da kayar baya ta kasar.

Tun bayan harin, hukumomin Bangladesh suka dinga dirar mikiya ta ba sani ba sabo kan masu tayar da kayar baya, da nufin karya su a kasar da Musulmai ne mafi yawa.

Da yake magana bayan yanke hukuncin, mai shigar da kara na gwamnati Golam Sarwar Khan, ya ce an samu hujjoji sosai kan tuhume-tuhumen da ake wa wadanda ake zargin.

"Kotu ta yanke musu hukunci mai tsanani,'' ya shaida wa manema labarai.

Ana zargin mutanen bakwai da aka yankewa hukuncin, da kasancewa mambobin wata kungiya da ta keta dokar kasa ta Jamaat-ul-Mujahideen Bangladesh (JMB).

A yayin da aka yanke musu hukuncin a Dhaka ranar Laraba, sun yi ta kabbara suna "Allahu Akbar (Allah Mai Girma)" a lokacin da ake fitar da su daga cikin kotun, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Yaya harin ya faru?

A yammacin ranar 1 ga watan Yulin 2016, 'yan bindiga biyar suka shiga kantin shan shayi na Holey Artisan a gundumar Gulshan na Dhaka.

'Yan bindigar masu dauke da bindigogi da adduna sun bude wuta suka kuma yi garkuwa da mutanen da ke cikin kantin.

Maharan sun kashe mutane da dama wadanda yawancin su baki ne 'yan kasashen waje, ta hanyar harbinsu ko yanka su.

An kira dakarun soji bayan da aka kashe 'yan sanda biyu masu fada da 'yan bindigar.

Bayan shafe sa'a 12 ana fafatawa, sojojin sun dirar wa ginin suka kuma ceto mutum 13 da aka yi garkuwa da su, sannan suka kashe 'yan bindigar biyar da suka kai harin.

Cikin wadanda suka mutun akwai 'yan kasar Italiya tara da 'yan Japan bakwai da wani Ba'amurke da wani dan Indiya.

Da take jawabi ta talbijin a lokacin da abin ya faru, Firai Minista Sheikh Hasina a lokacin ta ce: "Wadanne irin Musulmai ne wadannan mutanen? Ba su da wani addini. Wannan harin rashin imani ne."

Me hukumomi suka yi?

Jami'ai sun ce an kashe fiye da masu tsaurin addini 100 an kuma kama wasu kusan 1,000 a wasu samame da aka yi ta kai wa bayan harin.

Kafin sannan dai an sha kai munanan hare-hare kan masu rubutu a intanet da marubutan da babu ruwansu da addini da kuma mambobin 'yan tsirarun addinai.