Jagororin masu boren farashin man fetur 100' sun shiga hannu a Iran

Asalin hoton, Reuters
Hukumomin shari'a a Iran sun ce sun kama jagororin masu bore kan hauhawar farashin man fetur su kimanin 100 a kasar.
Wata sanarwa da ma'aikatar shari'a ta fitar ta ce rundunar sojojin kasar mai karfin iko ta Revolutionary Guards ce ta zakulo su "a sassan kasar daban-daban"
Matakin ya biyo bayan saka takunkumi da Amurka ta yi wa ministan sadarwa na kasar saboda dode hanyoyin sadarwa na intanet a yayin da ake boren.
Amnesty International ta ce an kashe fiye da mutum 100 a lokacin gumurzun da ya faru a biranen kasar masu yawa.
Amma hukumomin Iran sun ce mutum 12 ne suka rasa rayukansu.
Shugaba kasar ya yi wani jawabi ranar Laraba, wanda a ciki yake cewa kasar ta "sami nasara kan wani shirin da makiya suka kitsa", kuma ya ce Amurka, da Isra'ila da Saudiyya ne suka shirya tashin hankalin.







