Wane ne David Lyon, sabon gwamnan Bayelsa?

Asalin hoton, @iamLyondavid
A karon farko a tarihin siyasar jihar Bayelsa da ke kudu masu kudancin Najeriya, dan wata jam'iyyar ba na babbar jam'iyyar adawa ta PDP ba ya yi nasarar zama gwamna.
A ranar litinin ne hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ayyana David Lyon a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.
Lyon dan jam'iyyar APC ya yi nasara da kuri'u 352,552, kashi 25 cikin 100 na kuri'un da aka kada a kananan hukumomi takwas da ke jihar.
Shin wanene David Lyon?
David Lyon Pereworimi shi ne shugaban kamfani mai zaman kansa da ke samar da tsaro da masu gadi a jihar Bayelsa.
Ya kuma fito daga kabilar Olodiana da ke kudancin karamar hukumar Ijaw a jihar.
Mr Lyon ka iya zama sabuwar fuska ta fannin siyasa, to amma yana da 'yan kudade a hannunsa.
Ya tsaya takarar sanata mai wakiltar mazabar Ijaw ta kudu karkashin jam'iyyar PDP a shekarar 2011.
Amma a shekarar 2015 David Lyon ya fice daga jam'iyyarsa ta PDP ya komawa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Ya yi karatun firamare a makarantar Saint Gabriel da ke Olugbobiri daga shekarar 1978 zuwa 1983, daga nan ya tafi makarantar Sakandare a Olugbobiri daga shekarar 1984 zuwa 1988.
Ya kamalla karatunsa a kwalejin ilimi da ke jihar Rivers, inda ya karanta fannin koyarwa.










