Ana gab da sanar da sakamakon zaben mazabar Dino

Tun bayan wayewar garin ranar Lahadi ne aka dora kan aikin tattara sakamakon zabe daga kananan hukumomin jihar Kogi da ke arewacin Najeriya.

Masu sa-ido kan zabe sun yi zargin cewa an yi magudi a zaben ta hanyar sayen kuri`a da firgita masu zabe, lamarin da ka iya shafar sahihancin sakamakon zaben.

Yanzu haka dai hankali ya koma hedikwatar hukumar zabe ta kasa da ke Lokoja domin ganin yadda za ta hada alkaluma, kana ta sanar da sakamakon zaben gwamna, wanda aka kammala jiya.

An bude cibiyar tattara sakamakon zaben Bayelsa

Sakamako na kananan hukumomi 5 daga mazabar majalisar dattijai ta Kogi ta yamma sun kammala.

Yanzu haka ana jiran sakamako daga kananan hukumomi 2 ne domin tantance wanda ya lashe zaben sanata tsakanin dan takara na jam'iyyar APC Smart Adeyemi da kuma Dino Melaye na jam'iyyar PDP.

Sakamakon da ya kammala ya hada da na kananan hukumomin Kabba/Bunu, da Ijumu, da Kogi Koton Karfe, da Mopa Muro, da kuma Yagba East.

An sake zaben mazabar majalisar dattijai ta Kogi ta tsakiya ne a ranar Asabar, bayan da kotu ta soke zaben da aka yi wa Dino Melaye a babban zaben Najeriya da ya gabata.

Yadda ake tattara sakamakon zaben gwamna.

An bude cibiyar tattara sakamakon zabe ne a Lokoja da ke jihar Kogi da misalin karfe 9 na safe.

A jihar Bayelsa ma an bude zauren tattara sakamakon zaben gwamna.

A ranar Asabar an samu rahotanni fara zaben a makare a wasu rumfunan zabe na jihar.

Guyawun masu sa-ido sun yi sanyi

Masu sa-ido a kan zaben da dama sun bayyana cewa an samu yamutsi a rumfunan zabe a wasu yankuna jihar Kogi, musamman ma yadda 'yan banga suka ringa cin karensu babu babbaka.

Sun ringa harba bindiga domin tarwatsa jama'a, suna kuma fasa akwatunan zabe, sun kuma sace wasu.

A wata mazabar ma, irin Adankolo da ke gefen birnin Lokoja, mutum uku ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai, wadanda BBC ta tarar ana kokarin yi musu jana'iza.

Abinda masu sa-ido suka ce?

Farfesa Jibrin Ibrahim, jami`i ne na cibiyar bunkasa demokuradiyya ta CDD da ke sa ido a kan zaben:

"Ana nuna karfin tuwo a wurare da yawa ko ma a hana zaben, a kori mutane, ko ma a kwashe kayan zaben."

Ya kara da cewa: "Abin da ya fi ba mu mamaki shi ne yadda aka bar 'yan banga na yawo da motoci a cikin jihar ba tare da jami'an tsaro sun dauki mataki a kansu ba."

Hukumar zaben Najeriya ta tabbatar da afkuwar wasu daga cikin aika-aikar, wasu kuma ta ce za ta bincika. Yayin da rundunar `yan sandan Najeriya ta ce jami`anta sun yi abin kirki, kasancewar sun bayar da kariya ga kashi casa`in cikin dari na jihar Kogin.

Ganin yadda rikici ya dabaibaye wannan zaben gwamnan, BBC ta tuntubi Alhaji Bala Salisu, wani jigo a jam`iyyar APC domin jin ko za su rungumi kaddara su amince da duk yadda sakamakon zaben ya kasance?

"Babu wata kaddara da za mu runguma da ta wuce cewa wannan tafiya Allah Ya riga ya bai wa Bello."

Shi ma Alhaji Baba Sule, jigo a jam`iyyar PDP cewa ya yi za su amince da sakamakon zaben, amma da sharadi:

"Idan aka bi tsari yadda doka ta ce, tabbas za mu amince da sakamakon zaben."

Mutum 23 ne ke takarar kujerar gwamna a zaben gwamnan Kogi, amma gwamna Yahaya Bello na jam`iyyar APC da Musa Wada na jam'iyyar PDP da kuma Natasha Akpoti ta jam'iyyar SDP su ne a sahun gaba.