Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Na tono gawar mahaifana don sayar da kasusuwansu kan $300'
'Yan sanda a Mozambique suna tsare da wani mutum a yankin Nampula da ke arewacin kasar, wanda ake zarginsa da tono gawarwakin iyayensa da kawunsa don cire kasusuwansu.
Mutumin ya shaida wa 'yan sanda cewa wani attajirin dan kasuwa ne ya yaudare shi da yi masa alkawarin ba shi babur da kuma dala 300.
Dan kasuwar dai yana yin harkokin da suka shafi hakar ma'adinai ne a garin Lalaua da ke yankin, a cewar mutumin.
Ya amsa laifinsa a gaban 'yan sanda cewar shi kadai ya tono gawarwakin a dare daya.
An kama mutumin ne a kauyen Ntocol da ke kan iyakar gundumar Lalaua and Mecuburi.
Ya shaida wa BBC cewa: "Dan kasuwar ya ce min ne nemo kasusuwan mutanen da suka mutu ba tare da sun yi jinya ba. Idan na yi haka zai ba ni babur."
"Sai na tafi makabartar da ake binne danginmu, na tono kaburburan mahaifina da mahaifiyata da kawuna na ciro kasusuwansu. Sai na bar Lalaua. Amma ban yi sa'ar zuwa na samu dan kasuwar ba."
Ana tsare da mutumin a ofishin 'yan sanda da ke yankin Nampula inda ake ci gaba da bincike.
Mai magana da yawun 'yan sanda Zacarias Nacute ya shaida wa BBC cewa wannan ne karo na biyar da aka samu irin wannan lamari a yankin cikin shekarar nan.
Ana yawan alakanta irin hakan da tsafi.