Yadda wani ya daba wa masu casu wuka a Saudiyya

Lokacin karatu: Minti 2

Jami'an tsaro a Saudiyya sun kama wani mutum da ya daba wa wasu 'yan rawa guda uku wuka.

An bayyana cewa mutanen sun samu rauni a harin wanda ya faru a dandalin casu da ake gudanarwa a Riyadh don nishadi, wani sabon al'amari ga wasu 'yan kasar wanda a baya haramtacce ne.

Wani bidiyo da ke yawo a kafofin sadarwa na intanet ya nuna yadda 'yan rawa ke cashewa, sanye da tufafi masu kyalkyalin zinari, sai kwatsam ba zato ba tsammani, wani mutum ya zaro zungureriyar wuka da tsawonta ya kai santimita 30 ya abka wa tawagar da ke casun kan dandali.

Daga bisani mutumin ya zame ya fadi, sai kuma jami'an tsaro suka shiga tsakani.

Wannan shi ne bidiyon da ya tavyawo a kafafen sada zumunta na Saudiyya kan yadda harin ya faru.

Maza biyu da mace daya ne maharin ya yanka da wuka, amma an ce ba su ji rauni ba sosai.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya bayyana maharin a matsayin dan shekara 33 dan asalin kasar Yemen.

Ba a bayyana manufarsa ba ko dalilin da ya sa ya kai harin.

Ana gudanar da casun ne a Dandalin Sarki Abdallah, kuma bikin ya kasance daya daga cikin casun da ake gudanarwa na tsawon wata biyu.

Hukumomin Saudiyya sun ce suna son samar da kudin shiga dala biliyan 64 daga bangaren nishadi daga cikin matakan rage dogaro da arzikin fetur.

Shekarun baya dai wani ba zai taba mafarkin za a gudanar da irin wannan casu ba a Saudiyya, amma yarima mai jiran gado Mohammad Bin Salman ya kawo sabbin sauye-sauye.

Sauye-sauyen sun hada da bude gidajen sinima tare da kashe kudade wajen hada casu ga manyan mawaka irinsu Janet Jackson da shirya damben zamani na maza da mata da kuma bai wa mata izinin tukin mota.

Sabbin sauye-sauyen sun fusata wasu malaman kasar, sai dai suna samun karbuwa daga matasan Saudiyya.