Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mace ta kashe kanta don kyamar da mijinta ke yi wa bakar fatarta
'Yan sanda a Indiya sun ce wata mata mai shekara 21 ta kashe kanta saboda tsangwamar da mijinta yake yawan yi mata cewa ita baka ce.
'Yan sandan yankin Rajasthan sun shigar da karar mijin matar bayan da mahaifinta ya kai karar mijin kan zargin laifin kashe ta.
'Yan sanda sun sanar da sashen Hindi na BBC cewa har yanzu ba a kama kowa ba kan zargin. Har yanzu mijin nata bai ce komai ba kan lamarin.
Da yawan 'yan Indiya na ganin cewa samun hasken launin fata daukaka ce kan bakar fata.
Mahaifin matar ya shaida wa 'yan sanda cewa mijin 'yarsa na "wulanta ta saboda fatarta baka ce" wanda hakan ya yi sanadin da ta kashe kanta.
Wannan ba shi ne karon farko ba da nuna kyamar "bakar fata" ya yi sanadin da mata ke kashe kansu a Indiya ba.
Wata mai shekara 29 ta kashe kanta a 2014 bayan da mijinta ya nuna kyama kan launin fatarta a cewar 'yan sanda.
A shekarar 2018, wata 'yar shekara 14 ta kashe kanta bayan da 'yan ajinta suka tsangwameta inda suka kira ta"mummuna" saboda ita "baka' ce.