Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Iran ta 'samu rijiya mai gangar danyen mai biliyan 53'
Shugaban Iran, Hassan Rouhani ya fadi cewa kasarsa ta sake samun wata rijiyar mai wadda za ta kara wa kasar yawan man da kaso daya bisa uku na yawan man da kasar take hakowa.
Rijiyar man wadda take kudu maso yammacin lardin Khuzestan na da girman da ya kai mil 926, inda kuma take kunshe da gangar danyen mai biliyan 53.
Iran dai ta dade tana fama da yadda za ta sayar da man nata a kasuwar duniya sakamkon tsauraran jerin takunkuman da Amurka ta kakaba ma ta.
Amurka dai ta kakaba wa Iran jerin takunkuman ne bayan Amurkar ta fice daga yerjejeniyar nukiliya da aka cimma da manyan kasashen duniya a 2015.
Hakan na nufin kudin shigar kasar ta fannin sayar da mai zai karu da dala biliyan 32 "idan aka fara hakar man ko da kuwa da kaso daya ne", in ji Rouhani.
"Ina shaida wa fadar White House cewa a dai-dai lokacin da ki ka sanya wa Iran takunkumin sayar da man, to ma'aikatanta da injiniyoyinta sun iya gano karin rijiyar mai mai yawan ganga biliyan 53," kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ta Fars news agency ya rawaito Rouhani na fadi.
Wannan rijiyar man ka iya zama mafi girma ta biyu ga kasar ta Iran, bayan wadda ke da gangar mai biliyan 65 a Ahvaz, in ji kamfanin dillancin labarai na AP.
Iran dai ita ce kasa ta hudu a duniya mai yawan mai sannan ita ce ta biyu a yawan iskar gas.
To sai dai shugaba Donald Trump na Amurka ya sake kakaba wa kasar jerin takunkuman tattalin arziki a 2018.
Takunkumin ya janyo tattalin arzikin Iran ya shiga halin dimuwa, inda darajar kudin kasar ta karye warwas sannan farashin kayyaki ya yi tashin gwauron zabbi, al'amarin da ya kori masu zuba jari.