Iran ta hana jamia'ar IAEA mai bincike shiga cibiyar nukiliya

Iran ta soke izinin da ta ba wata jami'ar hukumar da ke binciken ayyukanta na samar da makamashin nukiliya (IAEA) da ta so shiga wata cibiya a makon jiya.

Ta ce matar ta janyo hankali kan ta ne bayan da aka gano tana dauke da wata na'ura tare da ita da Iran ta ce "abu ne mai tayar da damuwa" kan manufar jami'ar.

Hukumar IAEA ta ki amincewa da matsayar Iran kan matakin da ta dauka kan jami'ar, kuma ta soki yadda aka tsare jami'ar na wani lokaci.

Iran ta hana matar barin kasar na wani lokaci.

Wannan ce takardama irinta ta farko tsakanin Iran da hukumar tun 2015 - lokacin da aka kulla yarjejeniyar nukiliyar Iran.