Gwamnati ta rufe dukkanin makarantun mari a Kano

Sheikh Muhammadu Aminu Abubakar mai makarantar mari a Unguwar Arzai a Kano ya ce shi ba tsoron kar hukuma ta kama shi da laifi ne ya sa ya rufe gidan ba.

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Jahar Kano a arewacin Najeriya ta bayar da umarnin rufe gidajen mari da ake da su a fadin jahar har sai ta fitar da tsarin da ya dace.

Shugaba kwamitin kula da makarantun tsangayu a jahar Dr Muhammad Tahar Adamu ne ya sanar da daukar matakin, kuma sanarwar da ya fitar ta ce matakin bai shafi makarantun islamiya da na allo ba a jahar.

A cikin sanarwar, gwamnati ta ce ta rufe gidajen ne don binciken yadda ake cin zarafi da take hakkin dan adam da ake zargin ana yi a gidajen marin.

"Ba wai an yi ba ne don danne wa wani hakkinsa," in ji sanarwar

Wannan matakin na zuwa ne bayan dirar mikiyar da 'yan sanda ke yi a kan gidajen marin da ake tsare "kangararru" a wasu sassa na kasar.

Ko a makon da ya gabata sai da kwamitin na kula da makarantun tsangaya ya rufe wata makarantar mari ta Daiba da ke rijiyar lemo tare da mika yaran da kwamitin ya sama cikin mari ga hukumar Hisbah.

Kwamitin ya ce gidajen za su ci gaba da kasance a rufe a fadin jihar har zuwa lokacin da gwamnati ta fitar da tsarin shari'a da sharuddan da za a tafiyar da gidajen na mari a Kano.

Kwamitin na Dakta Muhammad Tahar Adamu ya shawarci iyayen yara su je gidajen marin su dauki 'ya'yansu nan da kwanaki uku.

Sannan sanarwar ta yi kira ga al'umma su kai wa hukuma rahoton inda suka ga ana tafiyar da irin wadannan gidajen marin.