Adam Zango ya kashe N46m kan karatun marayu

Asalin hoton, Instagram/Adam Zango
- Marubuci, Habiba Adamu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 1
Shahararren tauraron fina-finan Hausa, Adam Zango ya biya kudin karatun wasu dalibai na shekara uku, inda ya kashe fiye da naira miliyan 46.
Mawakin ya wallafa takardar tabbatar da samun tallafin da ta fito daga makarantar Farfesa Ango Abdullahi da ke Zaria, a shafinsa na Instagram.
Haka kuma takardar ta nuna cewa ya biya kudin karatun yara 101 ne, wadanda yawancinsu marayu ne da kuma yaran da suka fito daga gidajen marasa galihu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram, 1
Bayanan da ke kunshe a takardar sun kuma nuna cewa Zango ya biya kudin karatun yaran ne tun daga aji hudu zuwa kammala karatunsu na sakandare.
Ko da yake tauraron fina-finan bai yi wani karin bayanin kan dalilan da suka sa ya yi hakan ba, wasu masu mu'amala da shafukan sada zumunta da ke yada hotunan takardun, sun bayyana cewa mataki ne mai kyau da ya kamata a yi koyi da shi.
Tuni dai wannan mataki na Adam Zango ya janyo martani a kafafen sada zumuta.
Babu karin bayanai
Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.Karshen labarin da aka sa a Facebook
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram, 2
Ba wannan ne dai karon farko da taurarin Kannywood ke tallafawa marasa karfi ba, sai dai a iya cewa wannan ne karon farko da wani tauraro ya yi irin wannan bajinta a lokaci daya.