An kori 'yar majalisa daga jami'a a Bangladesh

An kori Tamanna Nusrat daga jami'ar karatu daga gida a Bangladesh sakamakon hayar mutum takwas da ta yi don su rubuta ma ta jarabawa, kamar yadda jami'an jami'ar suka bayyana.

Tamanna Nusrat, dai 'yar majalisa ce daga jam'iyyar Awami League mai mulkin kasar, kuma tana karatun digiri na farko ne a jami'ar.

Lamarin ya faru ne bayan wata tashar talabijin din Bangladesh ta rutsa daya daga cikin wadanda suka zauna don rubuta jarabawar a lokacin da ake tsaka da yin ta.

Lokacin da BBC ta tuntubi Miss Nusrat kan batun ba ta ce komai ba, wadda daya ce daga cikin mata 'yan majalisa 50 a zauren majalisun kasar.

Wata tashar talabijin mai zaman kanta Nagorik, ta ce kawo yanzu tuni aka yi jarabawa 13 cikin zangon karatu biyu kuma babu ko daya daga ciki da 'yar majalisar ta halarta.

Shugaban jami'ar karatu daga gida na Bangladesh Farfesa M.A Manna shi ne ya sanar da hukuncin korarta da jami'ar ta yi.

A ranar Asabar da ta wuce ne dai gidan talabijin din Narsingdi ya bankado balullubar a kwalejin gwamnati inda daliban ke rubuta jarabawar.

Farfesa M.A. ya shaida wa jaridar Daily Sun ta kasar cewa ''An kore ta daga jami'ar kuma ba za a kara bari ta zana jarabawa a makarantar ba''.

Tuni aka kafa wani kwamiti na musamman da zai duba lamarin, da duba ko za a dauki mataki akan Miss Nusrat, ko wadanda suka zauna zana jarabawar ko kuma malaman kwalejin.

Miss Nusrat matar marigayi Lokman Hossain magajin garin Narsingdi da ke birnin Dhakais ce, wanda aka kashe a wani hari da 'yan bindiga suka kai a shekarar 2011.