'Gwaggon biri na yada maleriya mai kisa ga mutane'

Wani nau'in cutar zazzabin cizon sauro mai matukar hadari da ke kama birai ya fara kama dan adam, kamar yadda masana kimiyya suka gano.

Dubbai ne ke mutuwa a sanadiyyar kamuwa da cutar malaria a duk shekara.

Dangin gwaggon biri da ake samu a Afirka ne suka fara kamuwa da kwayar cutar.

To sai dai bayan shekaru dubu 50, a yanzu an gano kwayar cutar ta fara bazuwa ga bil'adama wadda kuma ta hanyarta ake sa ran samun wasu magungunan waraka daga cutar malaria.

Cizon Sauro

Bayanan da aka wallafa a mujallar PLoS Biology ana fatan za su taimaka wurin gano wasu sabbin hanyoyin yakar cutar Malaria.

Ana daukar cutar malaria ne ta sanadiyyar cizon sauro da ke dauke da kwayar cutar, yayin da ya harbi dan adam ko kuma dabba.

Masu bincike sun yi amanna cewa dubban shekaru da suka wuce an yi wasu nau'ikan cutar malaria guda biyu da suka addabi birai kuma suna da alaka da juna.

Jagoran masu gudanar da binciken Dr Gavin Wright ya ce cutar ba kasafai ake samun ta ba to amma a yanzu ta kashe mutane da dama ta kuma haifar da wasu cututtuka na daban.

Dr Gavin ya kuma sanar da cewa sun yi matukar mamaki da bayanan da suka samu kuma binciken da wasu masanan suka yi zai kara bayar da haske kan yadda wannan cuta ta bazu daga dabbobi zuwa mutane.

A yanzu dai maganin Rh5 aka dogara da shi a matsayin rigakafin cutar kuma akwai fatan binciken da masana ke yi ya kara fito da wasu hanyoyin kawar da cutar.

Sai dai a cewar Mr Gavin zai yi wuya cutar ta kara daukar wani salo wanda masana ba su gano ba a binciuken da suka yi duk da babu tabbacin haka dari bisa dari.

A yanzu dai kashi 50 ne na al'ummar duniya cutar malaria ke yi wa barazana.

Kuma mafi yawancin mace-macen da cutar ke haddasawa na faruwa ne a nahiyar Afrika daga nau'in kwayar da ake kira Plasmodium falciparum.